
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya NEMA,
Jihohin da za su fuskanci ambaliya sune ta yi gargaɗin cewa za a samu aukuwar wasu ambaliya a kogin Neja da kuma kogin Benue, sakamakon sake ruwa daga madatsar ruwa ta Lagdo da ke Jamhuriyar Kamaru.
Babban darektan hukumar, Mustapham Ahmed, shi ya yi gargaɗin a ranar Asabar a Abuja, inda ya ce tuni jihohi kamar Adamawa da Taraba da kuma Benue suka fara jin tasirin ambaliyar bayan sake ruwan madatsar Lagdo.
Jihohin da za su fuskanci ambaliya
NEMA ta yi kira ga jihohi da ke kusa da kogin Benue da kuma kogin Neja, da su zauna cikin shirin ko-ta-kwana, inda ta yi gargaɗin cewa ƙarin jihohi za su fuskanci ambaliya a kwanaki da ke tafe.