Labarai

JIHAR KANO; Yan Nijeriya Mazauna Landan Sun Nemi A Yi Wa Gwamnatin NNPP A Kano Adalci.

RANAR ‘YANCI: ‘Yan Nijeriya Mazauna Landan Sun Nemi A Yi Wa Gwamnatin NNPP A Kano Adalci

 

A wani ɓangare na murnar zagayowar Ranar Samun ‘Yanci shekaru 63 da Najeriya ta yi, ‘yan ƙasar mazauna Landan sun yi dafifi a Ofishin Jakadancin Najeriya da ke birnin Landan, inda su ka nemi a yi adalci a shari’ar zaɓen gwamnan Kano.

 

Sun taru a ofishin kowane ɗauke da kwali mai ɗauke da bayanan zargin cewa jam’iyyar APC a ƙarƙashin jagorancin tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ta yi katsalandan a shari’ar da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Kano ta yanke.

 

Sun riƙa ɗaga kwalaye masu ɗauke rubutu daban-daban, domin su isar da saƙon neman a yi shari’a bisa tsari na gaskiya tare da adalci ga gwamnatin NNPP a Jihar Kano.

 

Sun taru ne a ranar Lahadi, ranar da ta yi daidai da ranar zagayowar samun ‘yancin Najeriya.

 

Wasu daga cikin saƙonnin da ke rubuce a kwalayen sun haɗa da:

 

“Yancin kowace ƙasa dai ya dogara ne ga ‘yancin fannin shari’ar ta.”

 

“Kada fa a yi wa Kano fashi da ƙwacen mulki. Tinubu ya bari tsarin mulki da shari’a mai adalci ta wanzu a Kano, kuma ta yi tasiri a hukunci.”

 

“Tilas A Bar Wa Kano Abin Da Suka zaɓa, Ba Sauran Mulkin Rashin Adalci:Kada a sake a yi wa Abba ƙwacen nasarar zaɓen da ya yi.”

 

“Dole Ne Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓe Su Yi Adalci – kuma kada shari’ar zaɓen Kano ta zama zakaran-gwajin-dafin zalunci.”

 

“A Nesanta Siyasa Daga Cikin Kotunan Mu – Kotun Ɗaukaka Ƙarar Zaɓen Kano Ta Bi Son Ran Wasu!”

 

“Rashin nuna ɓangaranci ga masu shari’a shi ne jigon yanke hukunci. Kanawa sun cancanci a yi masu adalci da gaskiya, ba a siyasantar da hukuncin kotun zaɓe ba.”

 

“A Kare Dimokraɗiyya kuma a yi adalci a kotunan shari’un zaɓe. Kanawa sun cancanci a yi masu adalci.”

 

Jagoran masu jerin gwanon zanga-zangar, Dakta Aminu Bello, ya shaida wa ‘yan jarida cewa sun je Ofishin Jakadancin Najeriya da ke birnin Landan ne domin nuna rashin amincewa da hukuncin da Kotun Shari’ar Zaɓen Gwamnan Jihar Kano ta yanke, wanda ya haifar da matuƙar damuwa kan rashin adalcin da ake zargin an yi. Lamarin da ya haifar da kiraye-kirayen a yi gaskiya da adalci a Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Tarayya.

 

Bello ya ce hukuncin da Kotun Shari’ar Zaɓen Kano ta yanke ya jefa shakku a kan fa’ida da nagartar da ake tinƙahon samu a tsarin dimokraɗiyya.

 

Ya ce lallai kada a sake a ƙwace halastacciyar nasarar da Gwamna Abba Kabir Yusuf na NNPP ya samu.

 

A ƙarshe ya yi kira ga ƙungiyoyin kare haƙƙi da na dimokraɗiyya, jam’iyyun siyasa da ƙungiyoyin ƙasa-da-ƙasa su sa ido sosai a kan abin da ke faruwa a Kano.

 

“Kuma muna kira ga hukuma ta yi ƙwaƙƙwaran bincike tare da sake bibiyar yadda aka zartas da hukuncin shari’ar zaɓen gwamna a Kano, tare da hukunta duk alƙalin da aka samu ya bada kai borin wasu masu son shirya zalunci ya hau,” Inji Bello.