Labarai

Jami’ar Chicago Ta Tabbatar Certificate Din Bola Tinubu Na Bogi Ne.

Shugaba Tinubu Ya Buƙaci Kotu A Ƙasar Amurka Ta Sake Duba Hukuncinta Na Bada Umarni Ga Jami’ar Chicago Ta Bayyanawa Atiku Bayanan Karatunsa

 

Shugaban Nageriya Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci kotun ƙasar Amurka da ta sake duba hukuncin da ta yi na umartar Jami’ar Chicago akan ta ba wa abokin adawarsa na siyasa, Atiku Abubakar na PDP, bayanai akan takardunsa na shaidar gama makarantar.

 

Tinubu ya bayyana cewa hukuncin kotun majistiri na Jeffrey Glibert wanda ya bada umarni a ranar 19 ga Satumba, kan buƙatar Atiku ya saɓawa tanadin doka sashe na 1782 na dokokin shari’ar ƙasar Amurka.

 

Ƙarƙashin hakan ne kuma Tinubu ya nemi mai shari’a Nancy L. Maldonado da yin watsi da buƙatar Atiku Abubukar.