Labarai

Jami’ar Birtaniya za ta fara digiri na biyu a fannin tsafi

Jami'ar Birtaniya za ta fara digiri na biyu a fannin tsafi

Jami’ar Exeter da ke Birtaniya, ta ce digiri a fannin tsafi da sihiri da za ta fara a shekara ta 2024, zai kasance ɗaya daga cikin irinsa na farko a ƙasar.

 

Sabon digiri na biyun a fannin Kimiyyar Tsafi da Sihiri, an ƙirƙiro shi ne saboda ƙaruwar masu nuna sha’awa a bangaren, cikin ‘yan shekarun baya-bayan nan”, cewar shugabar kwas din.

 

Shugabanni a ɓangaren sun ce matakin zai ba da damar yin nazari kan tarihi da tasirin maita da kuma tsafi a duniya da alaƙar da al’ummomi da ma ilmin kimiyya.

 

Za a fara koyar da kwas din ne na tsawon shekara ɗaya, daga watan Satumban 2024.

 

Masana masu ƙwarewa a fannin tarihi da adabi da falsafa da kimiyyar kufai, ilimin zamantakewa da ilimin halayyar ɗan’adam da wasannin kwaikwayo da nazarin addini ne, za su fito da matsayin da tsafi ke da shi a ƙasashen Yamma da kuma na Gabashin Duniya.

 

Jami’ar ta ce yana ɗaya daga cikin kwasa-kwasan karatun digiri na biyu a Birtaniya, da zai ƙunshi nazarin tarihin tsafi da sauran ɗumbin darussa masu alaka.

 

Matsayin tsafi’

Farfesa Emily Selove, shugabar kwas ɗin, ta ce “Ƙaruwar sha’awar da ake nuna wa a baya-bayan nan kan kimiyyar tsafi da sihiri, a ciki da wajen cibiyoyin koyo da koyarwa, ta ta’allaƙa ne a kan wasu ginshiƙan tambayoyi da aka fi neman amsoshinsu a tsakanin al’ummominmu.

 

“Warware tasirin mulkin mallaka da zaƙulo wani madadin fahimtar ilimi da fafutukar kare haƙƙin mata da yaƙi da nuna wariyar launin fata, su ne tushen wannan karatu.”

 

Za a koyar da darasin ne a Cibiyar Nazarin Rayuwar Larabawa da addinin Musulunci.

 

Farfesa Selove ta ce: “Wannan digiri na biyu, zai bai wa mutane damar sake tunani game da abin da ake ƙaddarawa cewa Ƙasashen Yamma ne cibiya ko matattarar fifita tunani da kimiyya.

 

“Yayin da sauran duniya kuma suka kasance wurin da ake samun tsafi da camfe-camfe.”

 

Jami’ar ta ce digirin, zai koya wa ɗalibai yadda za su iya karantarwa da yin jagora a fagen ilmi.

 

Da goyon na-baya da ayyukan kayan gadon tarihi da na gidajen tarihi da aiki a ɗakunan karatu da cibiyoyin yawon shaƙatawa da ƙungiyoyin ayyukan fasaha ko maɗaba’un buga littattafai, da dai sauransu.

 

Zaɓin darussan da ɗalibi zai yi ya ƙunshi nazarin dodon diragon a adabin ƙasashen yamma da ayyukan fasaha da rayuwar Gwarzon Sarki Arthur.

 

Akwai ma nazarin hanyoyin rubutu na tun tale-tale da mahangar ilmin addinin Musulunci da ra’i ko hangen ilmin kufai da al’adu da hoton yadda ake kallon mace a Shekarun Farkon Karni na 13 da 14 da kuma na 15.