
Ina Tinubu ya shiga ?

ASALIN HOTON,TINUBU FACEBOOK
Wani abun yabawa da tsarin dimokradiyya yake da shi, shi ne neman bayanai kan abubuwan da suke faruwa daga ko wanne sassa na gwamnati.
Wannan ‘yanci babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta yi amfani da shi domin neman ƙarin bayani kan shugaban ƙasar, ko yana ina? wane hali yake ciki? me yasa ba a jin ɗuriyarsa?. Duka na cikin tambayoyin da PDP ke buƙatar amsarsu.
Tun bayan kammala taron Majalisar Dinkin Duniya da aka yi a kasar Amurka, shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu bai koma gida ba, kuma babu wata sanarawa daga fadar shugaban kasar game da inda yake kamar yadda aka saba fitarwa idan zai yi tafiya ko kuma idan ya dawo a wasu lokutan.
A makon da ya wuce ne aka gudanar dataron na babban zauren MDD karo na 78 a Amurka kuma shi ne ya fitar da Shugaba Tinubu daga Najeriya.
An kuma gabatar da taron a ranakun 18 zuwa 22 na wannan watan na Satumba, wanda bayan kammala shi kowanne shuguba ya nufi ind ya fito.
Jam’iyyar PDP ta ce bayan ci zama tsegumi ne, tun da an kammala taron kamata ya yi a ce shugaba Tinubu ya koma gida, sai ga shi an shafe kwanaki amma shiru kake ji.
Kuma ganin shirun ya yi yawa ne jam’iyyar ta ce bai kamata shugaban kasa ya yi irin wannan dogon nisan kiwon ba tare da fada wa `yan kasar ba, in dai ba wani abu ake boyewa ba.
Alhaji Ibrahim Abdullahi shi ne mataimakin kakakin jam’iyyar PDP na kasa ya kuma shaida wa BBC wannan wani sabon salo ne da zai iya sa ‘yan Najeriya a duhu.
“Ko wanne shugaban ƙasa ya gabatar da matsalar da ta shafi ƙasarsa kuma ya koma gida, sai dai na Najeriya kawai shi ne ba mu gani ba, to shi yasa muke bincike.
“Yana ina? Ya ɓace ne daga inda aka ƙare taro? ko ko ya kamo hanya jirgin ne bai sauka a Najeriya ba? idan babu ko ɗaya cikin waɗannan tambayoyi to muna son mu ji labarin ina yake domin a matsayinmu na ‘yan ƙasa muna da haƙƙin sanin waɗannan,” in ji Alhaji Ibrahim.