Labarai

Hukuncin kisa da aka yanke wa ɗan sandan Najeriya na tayar da ƙura

Hukuncin kisa da aka yanke wa ɗan sandan Najeriya na tayar da ƙura

Hukuncin kisa da aka yanke wa wani ɗan sanda ya haifar da muhawara kan hukuncin kisa a Najeriya, wanda ba kasafai ake aiwatar da shi ba.

 

An yanke wa Drambi Vandi hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin kashe Bolanle Raheem, wata lauya da ke Legas.

 

Wani alƙalin babbar kotun jihar Legas ya same shi da laifin harbin Misis Raheem, wadda ke ɗauke da juna-biyun tagwaye a ranar Kirsimeti na shekarar 2022.

 

Misis Raheem ta kasance a cikin mota tare da mijinta da kuma wasu ’yan uwa yayin da suke dawowa daga coci lokacin da aka sami hatsaniya a shingen bincike tsakanin su da ‘yan sanda.

 

Ana ganin wannan hukuncin a matsayin wani muhimmin hukunci, inda a lokuta da dama ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama ke zargin ‘yan sandan Najeriya da sauran jami’an tsaro da cin zarafi, ƙwace da kuma kisa, lamarin da hukumomi ke musantawa.

 

A shekarar 2020, dubbban matasan Najeriya ne suka fito kan tituna domin nuna adawa da ta’asar da ‘yan sanda ke yi, bayan wani bidiyo da ya bazu na wani mutum da ake zargin jami’an tsaro na musamman na yaƙi da fashi da makami (Sars) sun kashe, lamarin da ya haifar da zanga-zangar #EndSars.

 

Zanga-Zangar ta kai ga gwamnati ta amince ta rusa rundunar ta Sars.

 

Amma yayin da alƙalai ke ci gaba da yanke hukuncin kisa, ba kasafai ake aiwatar da hukuncin ba a ƙasar da ta fi yawan al’umma a Afirka.

 

Najeriya na da sama da mutane 3,000 da aka yanke musu hukuncin kisa, a cewar ƙungiyar Amnesty, wanda shi ne mafi yawa a yankin kudu da hamadar Sahara.

 

Tsakanin shekarar 2007 zuwa 2017, an aiwatar da hukuncin kisa guda bakwai a ƙasar – huɗu a shekarar 2013, da kuma uku a shekarar 2016 saboda laifukan kisan kai da kuma fashi da makami – a cewar ƙungiyar.

 

Tun daga wannan lokacin, alƙalai sun sake yanke hukuncin kisa fiye da 500 – wanda na baya-bayan da aka yanke ya kasance a watan Yuli – bisa laifuka kamar cin amanar ƙasa, da yin garkuwa da mutane da kisan kai da fashi da makami da kuma tarayya da kungiyoyin ‘yan bindiga – wanda ya kasance gado ne da Najeriya ta yi daga zamanin mulkin mallaka.

 

A wasu jihohin arewacin Najeriya da ake amfani da shari’ar musulunci, akan yanke hukunci kisa kan laifukan da suka haɗa da zina da fyaɗe da luwadi da jima’i tsakanin shaƙiƙai da kuma maita.

 

Duk da cewa dokar Najeriya ta haramta yanke hukuncin kisa kan yara, amma a waɗannan jihohin ba a ɗaukar mutanen da suka balaga a matsayin yara, ko da kuwa ba su kai shekara 18 ba.

 

Misali shi ne batun Maimuna Abdulmumini wadda ta yi aure tana da shekara 13 kuma aka tuhume ta da laifin kashe mijinta aka yanke mata hukuncin kisa.

 

Bayan haka wata kotun Ecowas ta yanke hukuncin cewa Najeriya ta keta dokarta ta kare haƙƙin bil’adama ta kasa da kasa kafin a sako ta daga gidan yari a shekarar 2016.

 

Alhakin aiwatar da hukuncin kisa a Najeriya ya rataya ne a wuyan gwamnan jiha.

 

Galibin gwamnonin jihohi suna kaffa-kaffa da rattaba hannu kan hukuncin kisa saboda dalilan da suka shafi jin ƙai da siyasa da addini da kuma al’adu.

 

Shirye-shiryen daukaka ƙara wani lokaci kan ɗauki shekaru da dama kuma sau da yawa ana iya rasa takardun shari’ar, sai fursunoni su kasance cikin halin mummunar damuwa da tunanin mutuwa.

 

Duk da cewa tana da sassaucin ra’ayi, jihar Legas na da tarihin sauya hukuncin kisa zuwa ɗaurin rai da rai.

 

A baya dai jihar Delta da ke kudancin Najeriya ta yi afuwa ga fursunonin da aka yanke wa hukuncin kisa.

 

Vandi na da damar ɗaukaka ƙara – idan har aka tabbatar da hukuncin.

 

Gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu ne kaɗai zai iya bayar da umarnin zartar da hukuncin kisan.

 

Yayin da dokokin ƙasa da ƙasa suka amince da hukuncin kisa, ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama suna kira da a soke shi, ko kuma a dakatar da aiwatar da shi.

 

Aƙalla ƙasashe 112 ne suka soke hukuncin kisa kan dukkan laifuka a duniya.

 

A watan Yuli, Ghana ta soke hukuncin kisa kan duk wani laifi amma ban da cin amanar ƙasa, wanda ita ce ƙasa ta 27 a Afirka da ta ɗauki wannan matakin a cewar wata ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama mai suna ‘Coalition Against the Death Penalty’.

 

Saliyo ta soke hukuncin kisa a shekarar 2021.

 

A watan Yuli shugaban ƙasar Kenya William Ruto ya sauya dukkan hukuncin kisa da aka yanke kafin ranar 22 ga watan Nuwamban 2022 zuwa ɗaurin rai da rai.

 

Kafin wannan sanarwar, an aiwatar da hukuncin kisa na ƙarshe a ƙasar da ke gabashin Afirka a shekarar 1987, amma ana ci gaba da yanke hukuncin kisa duk shekara.

 

Yanzu a shekararta 21, ranar 10 ga watan Oktoba, ita ce ranar yaƙi da hukuncin kisa ta duniya.

 

Ƙungiyoyin fafutuka sun ce wannan rana na inganta tunani kan alaƙar da ke tsakanin hukuncin kisa da azabtarwa da kuma wayar da kan al’ummar duniya baki ɗaya kan lamarin.