Labarai

Hukumar Tace, “Ta Dauki Matakin Ladabtar Da Ma’aikaciyar Da Fursunan Da Aka Kama.

An kama Fursuna da ma’aikaciyar gidan yari suna baɗala.

 

Daga Al’ameen Minister yakasai

 

An dakatar da wata jami’ar hukumar kula da gidajen yari da aka gani a wani bidiyo tare da wani fursuna a gidan yarin Afirka ta Kudu suna lalata.

 

Mai magana da yawun hukumar gyaran tarbiyya ta kasar, Singabakho Nxumalo ya bayyana cewa tuni aka ɗauki mataki kan lamarin, wanda ake zargin ya faru a wani ofishi dake gidan Kula da gyaran hali na Ncome.

 

Bayyanar bidiyon ya janyo cece kuce tare da ɗumbin tambayoyi a zukatun jami’an hukumar na yadda fursunan ya yi amfani da waya ya ɗauki su bidiyo duk da cewa an hana amfani da waya a gidajen yarin ƙasar.

 

Singabakho Nxumalo ya faɗa wa gidan rediyo 702 na ƙasar a ranar Laraba 17 ga Maris, cewa za a hukunta ƙarin jami’an gidan yari idan aka sami hannun su cikin wannan laifi.

 

Jami’in yaɗa labaran hukumar ya ce, “Mun ɗauki matakin ladabtarwa akan ma’aikaciyar mu da wannan fursunan.