Labarai

Gwamnatin Biden ta ci gaba da gina katanga tsakanin Amurka da Mexico

Gwamnatin Shugaban Amurka Biden ta yi amfani da ikonta na zartarwa wajen tsallake wasu dokoki 26 na tarayya, don ci gaba da aikin gina katanga a iyakar kasar da Mexico, da zummar rage kwararar bakin haure.

Shugaba Biden dai ya yi ta sukar manufar tsohon shugaban kasar Donald Trump ta gina katanga lokacin da yake takara da shi a shekarar 2015.

Ɗaya daga cikin matakan da ya fara dauka a matsayinsa na shugaban ƙasa shi ne dakatar da gina katangar inda yayi alkawarin cewa a zamaninsa, babu sake yin almubazzaranci da sunan gina katanga.

Abun da ya sa a yanzu masu suka ke ganin ya yi amai ya lashe.

Umurnin zartarwa da ya bayar da nufin gina katangar a yanzu, na nufin hukumomi ba za su yi doguwar shari’ar kalubalantar keta dokokin kare muhalli ba.