Labarai

Gwamnan Jigawa Umar Namadi, Ya Kaddamar Da Sabbin Malaman Makaranta Guda 1,000.

Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi, ya kaddamar da sabbin Malaman makaranta guda 1,000 da ya dauka a fadin jihar Jigawa karkashin tsarin J-Teach ta ma’aikatar ilmi.

 

Gwamnan ya jagoranci taron kaddamar da sabbin Malaman ne a yau Talata a babban dakin taro na Ahmadu Bello da ke cikin sakateriyar gidan Gwamnatin jihar da ke Dutse, Jigawa.

 

Gwamna Malam Namadi, ya yi kira ga sabbin Malaman makarantar da su jajirce, su mayar da hankali wurin gudanar da aikin nasu, domin su bawa daliban jihar ingantaccen ilmi.

 

Gwamnan ya kara da cewa dukkannin wa ‘yanda aka dauka aikin, sai da suka rubuta jarabawa aka zabi wa ‘yanda suka fi chanchanta da kokari.

 

Amb Muhammad Salisu Seeker

Mataimaki na musamman ga Gwamnan jihar Jigawa a bangaren bugawa, da daukan hoto.