
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce ƙasarsa za ta janye jakadanta da ke Nijar tare da sojojinta da ke ƙasar da ke yankin Sahel, bayan juyin mulkin da sojojin na Nijar suka yi wa zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Mohamed bazoum.
Cikin wata hira da ya yi da gidan talbijin na ƙasar Mista Macron ya ce “Faransa ta yanke shawarar janye jakadanta da sauran ma’aikatan diplomasiyyarta domin komawa gida”.
Shugaba Macron ya ƙara da cewa aikin sojin ƙasar a Nijar ya zo ƙarshe, don haka sojojin kasar da ke aikin yaƙar masu iƙirarin jihadi a ƙasar za su koma gida nan da ‘yan watanni masu zuwa.
Ya ce za a fara janye sojojin ne mataki-zuwa mataki, kafin ƙarshen shekara lokacin da ya ce za a kammala kwashe dakarun daga ƙasar ta Nijar.
Shugaban na Faransa ya ce Faransa za ta tuntuɓi sojojin da suka kifar da gwamnatin shugaba Bazoum game da kwashe dakarun ƙasar, domin a cewarsa suna son janye sojojin ne cikin kwanciyar hankali da lumana.
Akwai dakarun Faransa kimanin 1,500 a Nijar da ke aikin yaƙar masu iƙirarin jihadi a yankin Sahel
Sojojin mulki na Nijar sun matsa lamba kan jakadan Faransa Sylvain Itte ya fice daga ƙasar bayan da suka kifar da gwamnatin Bazoum ranar 25 ga watan Yuli.
A cikin watan Agusta ne sojojin na Nijar suka bai wa Jakadan wa’adin sa’o’i 48 ya fice daga ƙasar, yayin da Faransa ta yi watsi da umarnin, sanna yi amincewa da gwamnatin sojojin.
A tattaunawar da gidan talbijin na Faransa, Mista Macron ya jaddada matsayin ƙasarsa na cewa sojojin Nijar sun yi garkuwa da shugaba bazoum, kuma shi ne kadai halastaccen shugabn Nijar.
Ya ce sojojin sun hamɓarar da shi ne saboda kawai sun ga ya dauko hanyar kawo auye-sauye masu muhimmanci a ƙasar.
Yankin Sahel da kudu da mhamadar sahara na fama da abin da Macron ya kira da annobar juyin mulki a ‘yan shekarun baya-bayan nan, inda sojoji suka maye gurbin shugabannin da aka zaɓa ta hanyar dimokradiyya a ƙasashen Mali da Burkina Faso da Guinea da Nijar.
Tun bayan juyin mulkin da sojojin na Nijar suka yi cikin watan yuli ne dai ‘yan kasar da dama ke gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga sojojin, tare da yin kiraye-kirayen ficewa Faransa daga ƙasar.