Faɗa Ko Gasar Technology Tsakanin China Da America
Faɗa Ko Gasar Technology Tsakanin China Da America
Me yake faruwa tsakanin America (iPhone 15 Pro Max) da kuma ‘kasar China (Huwaie Meta 60 Pro Max)?
_____________________________
Jiya Talata Kamfanin Apple 🍎 dake ‘kera wayoyin iPhone a America ya fitar da sabuwar wayar iPhone 15, mafi tsada a Tarihin wayoyin Kamfanin na Apple a jerin iPhone, akan Farashin 0.031 Bitcoin, ko Dala dubu 1,299 iPhone 15 Pro Max, wato kimanin Naira Miliyan 1,200,000 a Kudin Nigeria.
~ Anyi Bikin kaddamar da Wayar ne a California ta kasar Amurka.
Hakan yana zuwa ne a dai dai lokacin da aka fara gwabza fadan Technology tsakanin China da America cikin kwanaki hudu da suka wuce, bayan China ta fara ‘kera wani Chip da suka kira shi da (Kirin Chip) wanda Kamfanin zai yi amfani dashi akan wayar (Huwaie Meta 60 Pro Max) da ka iya doke iPhone 15.
~ Manyan Kamfanonin America da suke ‘kera Chip irin su AMD, Intel, Quan da TSMC sunce duk sun girgiza da suka samu labarin China tana kera Kirin Chip ta hannun Kamfanin Huwaie.
~ Sai dai ana ganin abu ne me wahalan gaske Kamfanin Huwaie shi kadai ya iya samar da Chip din da zai dauki 5G Network balle 6G, ana ganin ya hada kai da Kamfanin AMD da Intel ne wajen samarwa China da Chip din. Hakan yasa Amarica ta fara bincike da kafa Dokoki wa AMD da sauran kamfanonin da suke kera Chip kada su yarda su samar ko su bayar da taimako wa China akan Shirin ta na kera Kirin Chip.
~ Bayanan da suka tabbata a yanzu shine already China ta riga ta mallaki Kirin Chip.
~ Bayan Kamfanin Huwaie yayi alkawari da China zai taimaka mata ta mallaki Chip dinta da yasha babban da na kowa a duniya, har ma da Kamfanin AMD da Intel da TSMC.
~ Ba’a jima ba sai China ta fitar da sanarwa tana Haramta wa Ma’aikatan Kamfanoni da Ma’aikatan Gwamnatin ‘kasar mallakar iPhone, wanda hakan ya jawo Kamfanin Apple yayi asaran tsaban Kudi Dala Biliyan ‘dari biyu a cikin Awanni 48.
Sai dai China tace ta Haramtawa Ma’aikatan ta amfani da iPhone a kasar ne saboda security alert data samu, ganin cewa iPhone din tana dauke da 5G Network wanda ake ganin yana da matukan Hatsari ta bangarori da dama.
~ Bangare tsaro, sirri da bangaren lafiya.
Sai dai wasu suna ganin ba saboda tsaro bane China tayi haka wa Kamfanin Amarikawa na Apple, saboda ta fitar da Babbar wayar Huwaie Phone 📱 ne (Huwaie Meta 60 Pro) wacce akan ta ne aka fara amfani da Chip din da babu hannu ko fasahar America a ciki.
China tayi hakan ne domin karya kasuwar America a kasar ta dama duniya Baki ‘daya, babban abinda ya tayar da hankali shine yadda aka yi China ta fara kera Chip ba tare da sirrin ya fita ba. Dan haka ake ganin Huwaie Meta 60 Pro ta ninka iPhone 15 Pro Max.
~ Capacity din da China tayi Huwaie Meta 60 Pro yafi na iPhone 15 Pro Max da ninki Dari 780, sannan yana da tsarin 6G Network.
Haka kuma China ta Haramta wa Ma’aikatan Gwamnatin ‘kasar saya ko amfani da Motocin Kamfanin (Tesla) masu Lantarkin na Elon Musk wanda shima ‘dan American ne.
~ Samun damar kera “Kirin Chip” da China ta fara a yanzu, ana ganin shine targaden farko da America ta fara samu a bangaren fasahar kere kere a baya bayan nan.
America sun fitar da iphone 15 din ne a lamari me cike da sarkakiya da daure kai, anyi yunkurin dakatar da fitar da iPhone 15 har zuwa lokacin da za’a samu mafita akan kasar China, to amma bai yuwu ba tunda an dade da bayyana lokacin da za’a fitar da ita.
~ Bayan Awanni 24 da fitar da sanarwar da China tayi sai Kamfanin Huawei ya fitar da Huwaie Meta 60 Pro Max.
China dai bata tashi Haramta iPhone a kasar ta ba sai data tabbatar ta mallaki duk abinda take so na ‘kera Kirin Chip. Duk wata magana cewa China bata samu damar kera Kirin Chip ba babu kamshin gaskiya akai.
~ Me yasa America bata son China ta mallaki Chip din da yafi nata na Apple? shine saboda duk kasar data samu wannan damar to zata iya shan gaban America a wannan fagen.
Yanzu haka Huwaie yana ‘kera Kirin Chip mai 6G Network, wanda hakan yasa aka bar America a baya.
✍️:
Abdul-Hadee Isah Ibraheem.
12 September 2023.