Labarai

El-Rufai Ya Watsar Da Kujerar Minista Da Tinubu Ya Ba Shi.

DA DUMI DUMINSA: El-Rufai Ya Watsar Da Kujerar Minista Da Tinubu Ya Ba Shi

 

Daga Comr Nura Siniya

 

Tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai, ya yanke sha’awar cewa ba zai karɓi kujerar minista a gwamnatin Asiwaju Bola Tinubu ba, inda ya ƙaurace ma wata gayyatar da fadar shugaban ƙasa ta yi masa bayan dawowarsa daga ƙasar Netherlands a ƙwanan nan.

 

A ƙwanan baya “El-Rufai ya shaida wa Tinubu cewa, ya hakura da kujerar ministan, inda ya ce yana ji a jikin sa cewa aƙwai wasu mutane zagaye da shugaban Kasa da basu so ya zama minista.

 

Elrufa’i ya fadawa Tinubu cewa lokaci ya yi da ya kamata ya maida hankali wajen kasuwanci da karutun sa na digirin digir gir a Netherlands.

 

Hakan ya sa Tinubu ya maye gurbinsa a yau Talata inda ya tura sunan Balarabe Abbas daga jihar Kaduna a matsayin minista.

 

Sai dai kuma El-Rufa’i, ya yi wata magana mai harshen damo inda aka jiyo yana faɗan cewa Mu muka kai mune za mu dawo da shi, “wannan magana ta ɗaure kawunan ƴan Najeriya.