
Dakarun Faransa za su fara janyewa daga Nijar “a wannan makon”, in ji gwamnatin Paris a ranar Alhamis, bayan sun samu saɓani da gwamnatin mulkin soja tun bayan juyin mulkin watan Yuli.
Hedkwatar sojojin Faransa ta ce “Za mu fara aikin janye dakarun a wannan makon, cikin tsari mai kyau, cikin aminci da hadin gwiwa da Nijar.”
Sanarwar ta zo ne mako guda bayan da jakadan Faransa a Yamai, ya koma gida sakamakon matsin lamba daga gwamnatin kasar.
Shugaba Emmanuel Macron a ranar 24 ga watan Satumba dai ya ba da sanarwar janye sojojin Faransa 1,400″ a karshen shekara.
Sojojin Faransa sun kasance a Nijar a wani bangare na yaƙi da masu iƙirarin jihadi a fadin yankin Sahel.
Sojoji Kimanin 400 ne aka tura su aiki tare da sojojin kasar a arewa maso yammacin Nijar, kusa da kan iyaka da Burkina Faso da kuma Mali.
Yankin mai “iyaka uku”, ya yi kaurin suna a matsayin mafaka ga mayaka kungiya masu alaka da Alqaeda da IS.
Hedkwatar sojojin ta ce dakarun da ke janyewa daga yankin na buƙatar kariya kafin sun bar wuraren da aka jibge su, mai yiwuwa gami da tallafin jiragen sama daga babbar runduna a wani sansanin jiragen sama da ke wajen Yamai, babban birnin kasar.
Sojojin dai na cikin halin rashin tabbas tun lokacin da gwamnatin mulkin sojan Nijar ta fara neman janyewarsu tare da katse hanyoyin samun abinci, baya ga zanga-zangar kin jinin Faransa da kungiyoyin fararen hula suka rika yi a wajen birnin Yamai.
A yanzu dai sojojin Faransa za su janye ne ko dai ta kudu, hanyar Benin mai takun saka da gwamnatin mulkin sojan Yamai ko kuma ta Chadi daga gabas, wurin da hedkwatar dakarun Faransa da ke aiki a sahel take.
A yanzu haka, Yamai ta haramta zirga-zirgar jiragen Faransa a sararin samaniyarta.