Labarai

DA DUMI DUMIN: Sanata Mallam Shekarau Zai Kashe Makudan Kudade Don Gina School Of Hygiene Theater A Jihar Kanó 

DA ƊUMI-ƊUMI:

 

Sanata Mallam Ibrahim Shekarau Zai Kashe Naira Miliyan Ɗari Da Sha Biyar Domin Gina School Of Hygiene Theater A Jihar Kanó

 

DAGA Nura Kabaransi Gawuna.

 

Kabaransi Gawuna ya bayyana cewa shi ne ya nazama silar tabbatuwar wannan al’amari. Kamar yadda ya ce: “Allah nagode maka wata rana Dakta Bashir Getso ya kira ni har Office dinsa cikin Makaranta, ya ce suna so don Allah nayi magana da Maigirma Sardauna ta Hanyar Maigidanmu.

 

 

Alh. Murtala Yusuf SA Project, a taimakawa da makaranta ko gadar sama ta tsallaka titin ƴan makaranta ko ayi musu Laboratory room ko Thearter a cikin nakaranta kamar yadda Sanata Shekarau yayi a makarantar Health Tecnology na gina ajujuwa da Offices da Hall, nan take naje Office na Fadawa Maigirma Alh Murtala Bichi ya ce to ba komai.

 

Wata rana muna Abuja tare da Alhaji Murtala a Gidan Senator Shekarau Asokoro, sai na sake masa Tuni ai kuwa yana shiga Wajen Sardaunan Kano futowarsa ya ce Nura ka cewa Dakta Getso su rubuto abinda suke so a takardar, nan take na kira Shugaban Makarantar Hygiene Dr. Getso na sheda masa da wannan Albishir, nace masa ya rubuta takarda zan zo Kano na Amsa, kuma haka akayi ya Rubuto yabani nakaiwa SA Project, yau Kamar sati Biyu.

 

Dakta Getso ya kira ni a waya yake shaidamin Alh. Murtala ya kira shi ya faɗa masa Aikin nan da Sardaunan Kano ya shigar gaban majalisa aikin ya futo, yau kuma cikin Ikon Allah.

 

Daga baya saiga Hotuna daga Shekarau Digital Media ana ƙaddamar da wannan aiki, ga wakilin Sardaunan Kano nan Alh. Murtala SA Project, ga Dakta Bashir Getso nan a jibge kayan aiki an aza Harshashi”.