DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnati ta hana sayar da finafinai fassarar Indiya
DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnati ta hana sayar da finafinai fassarar Indiya
DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnati ta hana sayar da finafinai fassarar Indiya a Kano
HUKUMAR Tace Finafinai ta Jihar Kano ta dakatar da sayar da finafinai fassarar Indiya da ma sauran duk wani fim da aka fassara shi daga wani yare zuwa Hausa a dukkan faɗin jihar.
Shugaban hukumar, Alhaji Abba El-Mustapha, shi ne ya bayyana hakan a lokacin tattaunawar sa da mujallar Fim.
El-Mustapha ya ce: “Duba da yadda yanayin fassarar da ake yi da kuma tsarin finafinan mu ka ga ya zama dole a dakatar da sakin su har zuwa lokacin da za a yi gyara a kan tsarin da kuma samar da hanyar da ya kamata a fitar da shi.”
Ya ƙara da cewa, “Mu mutanen Jihar Kano mu na da tsari da kuma tarbiyya, don haka dole mu kula da abin da za a shigo mana da shi don ya zama bai yi barazana ga tarbiyyar mutanen jihar mu ba. Don haka mun kira masu gudanar da harkar fassara da kuma sayarwa domin mu ba su tsare-tsaren mu wanda za su tafi a kan su, sannan mu ji matsalolin su don mu ga ta ina za mu samar musu da maslaha.
Amma dai irin waɗannan finafinai fassarar Indiya da sauran su, ba za mu bari a ci gaba da tafiya a yanayin da ake ba. Za mu kawo gyara da kuma tsari domin tsaftace finafinan da jama’ar mu za su kalla ko namu na gida ko na waje.
“Don haka mu na kira ga masu yin harkar da su sani mu gyara mu ka zo; duk wanda ya ke son gyara ya zo mu tafi tare, wanda kuma ba ya son gyara, to da man na faɗa tun a baya ya fita ya bar cikin mu.”
Mun tambayi shugaban kungiyar masu fassarar finafinan Indaya da kuma sayar da su na Jihar Kano, Auwal Badi, a kan ko ya su ka ji da wannan sanarwar?
Sai ya ce: “To lallai mun samu wannan sanarwar, kuma an aiko mana, a yanzu mun san halin da ake ciki. Kuma mu na goyon bayan wannan doka. Kamar yadda hukumar ta ce za ta yi gyara ne, to mu na goyon bayan duk wani gyara da zai kawo mana cigaba a harkar kasuwancin mu.
Don haka za mu bai wa Hukumar Tace Finafinai dukkan goyon bayan bayan da ta ke buƙata domin samun nasara a Jihar Kano.”