Labarai

DA ƊUMI-ƊUMI: An Buƙaci DSS Da Ƴan Sanda Su Binciki Abba Gida-gida

DA ƊUMI-ƊUMI: An Buƙaci DSS Da Ƴan Sanda Su Binciki Abba Gida-gida

 

Wasu magoya bayan NNPP da Abba gida gida sun gudanar da zanga-zangar adawa da bangaren shari’ar Najeriya a birnin Landan a ranar Lahadi, 1 ga watan Oktoba An zargi gwamnan Kano da aka tsige da shugabancin NNPP da daukar nauyin zanga-zangar na birnin Landan.

 

An caccaki Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano da jam’iyyar NNPP kan gudanar da zanga-zanga a birnin Landan a ranar Lahadi, 1 ga watan Oktoba kan hukuncin alkalan kotun zaben gwamnan jihar.

 

Ku tuna cewa a ranar Laraba, 20 ga watan Satumba, kotun zaben ta ayyana dan takarar jam’iyyar APC, a zaben gwamnan jihar Kano da aka yi a ranar Asabar, 18 ga watan Maris, Nasir Gawuna, a matsayin wanda ya lashe zabe.

 

Yayin da take jawabi ga manema labarai a Abuja a ranar Litinin, 2 ga watan Oktoba, sakatariyar kungiyar ta kasa, Barista Isabella Odunayo, ya yi kira ga Sufeto Janar na yan sanda da hukumar DSS da su binciki Gwamna Yusuf da shugabancin NNPP kan zanga-zangar na Landan, kamar yadda Legit ta ruwaito.