Labarai

Cutar Diphtheria Ta Kashe Yara 117 A Yobe

Cutar Diphtheria Ta Kashe Yara 117 A Yobe

Cutar Diphtheria Ta Kashe Yara 117 A Yobe

Kananan yara 117 sun rasu a Jihar Yobe a sakamakon kamuwarsu da annobar cutar Diphtheria mai sarke numfashi.

Diphtheria yara Yobe

    DagaSani Saleh Chinade, Damaturu

Kananan yara 117 sun rasu a Jihar Yobe a sakamakon kamuwarsu da annobar cutar Diphtheria mai sarke numfashi.

Hukumar kula da lafiya a matakin farko ta kasa (NPHCDA) ta ce yaran sun rasu ne daga shekarar 2022 zuwa 2023, ko da yake yara 1,600 sun warke daga cutar a cikin tsawon lokacin.

Babban daraktan hukumar, Dokta Faisal Shuaib, ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ziyarci cibiyar killace masu cutar amai da gudawa da ke Potiskum.

Ya ce an muutm 1,796 ne suka kamu da cutar a Jihar Yobe daga ranar 22 ga watan Nuwamba 2022, kuma yara ’yan tsakanin shekaru 5 zuwa 14 ne akasarinsu.

Shu’aib wanda ya jagoranci kwamitin bayar da agajin gaggawa kan cutar Diphtheria zuwa jihar, ya bayyana jin dadinsa da allurar rigakafin da aka yi a Potiskum da kananan hukumomi 17 na jihar.

“Ya zuwa ranar 12 ga Oktoba, za a samar wa yara karin alluran rigakafin cutar da ke da matukar karfi wajen dacewa a rikafin.

Ya yi nuni da cewa, karancin allurar rigakafi ne ya haddasa bullar cutar a fadin kasar nan.

Shu’aib ya ce duk da cewa jihar Kano ce ta biyu a yawan masu fama da cutar diphtheria, amma kula da tsaftar muhalli da na mutum zai iya kawar da cutar cikin sauki.

Babban daraktan ya yabawa jihar Yobe da takwarorinsu  bisa rawar da suke takawa wajen magance cutar amai da gudawa, inda ya yi alkawarin ci gaba da tallafa wa jihar a fannin kiwon lafiya.

Ya ce, duk da haka, ya ce akwai bukatar samar da sashin kulawa mai zurfi wanda za a iya tuntubar masu fama da cutar mashako (diphtheria) don kulawa da kyau.