Labarai

China za ta ci gaba da aikin titin jiragen kasa a Najeriya

China za ta ci gaba da aikin titin jiragen kasa a Najeriya

Gwamnatin China ta amince da komawa cikin yarjejeniyar karasa aikin shimfida titin jiragen kasa daga Abuja zuwa Kano da kuma wanda ya tashi daga Fatakwal zuwa garin Maiduguri.

Wani mutum a kusa da wani jirgi dake shirin tashi daga tashar jiragen kasa dake birnin Legas zuwa Kano a tarayyar Najeriya. AP – Sunday Alamba

Shugaban China Xi Jinpin ne ya yi wannan alkawari ranar Laraba a birnin Biejing, bayan ganawa da mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima.

A zamanin gwamnatin da ta gabata Najeriya ta kulla yarjejeniya da China kan aikin samar da kudade da kuma shimfida manyan titunan jirgin kasan guda biyu, sai dai tun bayan bikin kaddamar da aikin hadin gwiwar Chinar ba ta saki kudaden da ta yi alkawarin bayar w aba, saboda wasu dalilai.

A halin yanzu dai kasar Sin din ta amince da bayar da kaso 85 na kudaden da ake bukata wajen aikin shimfida layukan dogon biyu, yayin da gwamnatin Najeriya za ta bayar da kashi 15 na kudaden ayyukan da ake bukata.