
Buhari ya taya Yana tayaku Murnan Yanci,
Tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya miƙa sakonsa na murnar bikin cika samun ƴancin kai ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma al’ummar Najeriya.
Wata sanarwa da mai magana da yawun tsohon shugaban, Malam Garba Shehu, ya fitar, ta ce Buhari na taya ƴan Najeriya murna da cika shekara 63 da samun ƴancin kai.
“Tsawon shekaru 63, Najeriya na ci gaba da zaburar da sauran ƙasashen nahiyar Afrika ta hanyar kirkire-kirkire da kuma ɗorewar mulkin dimokuraɗiyya,” in ji Buhari.
Ya ce yana da ƙwarin gwiwar cewa dimokuraɗiyya a matsayin tsarin gwamnati, za ta ci gaba da samun karfi a Najeriya.