Labarai

Budurwar da Aka Sace a Zaria an Mata kisan gilla

Budurwar da Aka Sace a Zaria an Mata kisan gilla

Mutane a birnin Zariya sun auka cikin alhini da kaɗuwa kan wani mummunan kisan gilla da aka yi wa wata budurwa ‘yar shekara 20, bayan an sace ta, sannan aka yi mata fyaɗe.

 

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce ta kama wani matashi ɗan shekara 27, lokacin da ya je karɓar cikon kuɗin fansa na marigayiya Fatima Adamu.

 

Suna zargin matashin ne da sace Fatima, sannan ya yi garkuwa da ita tsawon kwanaki, tare da karɓar kuɗin fansa, kafin ya halaka ta bayan ya yi mata fyade.

 

Tun farko, wani bidiyo ne da aka wallafa a shafukan sada zumunta, ya nuna wani matashi tare da wasu mutane, lokacin da yake tonon wani abu da aka binne.

 

Bidiyon ya nuna matashin yana haƙar wani abu mai kama da kabari a cikin ɗaki kuma aka ji inda yake nuna wani sashe na ramin, yana cewa ga alamar hannu nan.

 

A cikin wani bidiyon kuma, an ji muryar wani mutum lokacin da yake umartar matashin, ya fito da marigayiyar daga cikin kabarin. Daga nan sai ya kamo sashen hannunta ya tashi gawar zaune. Har a lokacin hannunta na bankare ta baya, ga alama ɗaure da igiya.

 

Al’amari ne mai matukar tayar da hankali da dugunzuma zuciya.

 

‘Yan sanda sun yi zargin cewa matashin ya kashe Fatima Adamu ne ta hanyar amfani da muciya, lokacin da yake tunanin yadda zai yi da ita, kafin dawowar iyalinsa, da suka yi tafiya.

 

Mai magana da yawun ‘yan sanda a Kaduna, ASP Mansur Hassan ya ce tun da farko, matashin da ake zargi ya karɓi kuɗin fansa naira 120,000 daga hannun mahaifan Fatima.

 

Kuma daga bisani ya nemi su cika kuɗin da ya nema kafin ya sake ta.

 

Jama’a da yawa har a shafukan sada zumunta, na ci gaba da bayyana ra’ayoyi kan irin tashin hankalin da suka shiga, sanadin wannan mugun labari.

 

Pharm Musa A. Bello a shafin Facebook ya ce hankalinsa ya tashi, zuciyarsa ta sosu, sannan yana cike da ɓacin rai.

 

A cewarsa, irin wadannan munanan ayyuka kaɗai sun isa jefa al’umma cikin halin ha’ula’i.

 

Allah ya kare mu da dukkan zuri’armu daga munanan ayyuka da sharrin mutane da aljanu, ya yi addu’a

Rundunar ‘yan sandan Kaduna ta ce daga binciken farko-farko da ta gudanar, Fatima ta shafe tsawon kwana hudu tsare a hannun matashin da ya yi garkuwar da ita.

 

Ta ce bayanan sirrin da ‘yan sanda suka samu a kan lamarin da ke faruwa game da garkuwar da aka yi da budurwar ne ya sanya su daukar matakai.

 

A cewar mai magana da yawun rundunar, sun kama matashin ne lokacin da ya je wurin da aka yi da shi, don karbar naira 80,000, a matsayin cikon kudin fansar Fatima.

 

Har lokacin in ji ASP Mansur iyaye da dangi ba su da masaniyar cewa matashin ya riga ya kashe Fatima har ma ya nemi wani daki a gidansa da ke unguwar Madaci, ya tona rami da shebur inda ya binne ta.

 

Ya ce zuwa yanzu daga bincikensu, sun fahimci cewa akwai yiwuwar da ma can matashin ya san Fatima kafin ya sace.

 

“Wannan ya sanya muke gudanar da sahihin bincike domin mu tabbatar da ainihin abin da ya kai ga sacewa tare da yin gakuwa da Fatima”.

 

“Ka ga wannan yake nuna mana, akasarin ayyukan da ake aiwatarwa na ta’addanci, mutanen da suke kusa da mu… Mutanen da suke kusa da al’umma, su ne suke bayar wadannan bayanan sirri ga masu laifi, ko kuma su zo su aiwatar da laifin sannan su zo cikin jama’a su labe.”

 

Mai magana da yawun ‘yan sandan ya ce duk wanda suka samu da hannu a binciken da suke yi, za su tabbatar sun kamo shi don kammala bincike kafin gurfanar da su a gaban kotu.

 

Ya kuma ce tuni rundunar ‘yan sanda ta ba da gawar marigayiyar ga mahaifanta inda su kuma su yi mata jana’iza tare da binne ta.