Bellingham ya kara tabbatar da Real Madrid a kan teburin La Liga
Bellingham ya kara tabbatar da Real Madrid a kan teburin La Liga

Bellingham ya kara tabbatar da Real Madrid a kan teburin La Liga

Jude Bellingham ya ci gaba da taka rawar gani da fara kaka a Real Madrid, wanda ya ci kwallo biyu a wasan da suka doke Osasuna.
Ƙungiyoyin biyu sun kara a fafatawar mako na tara a babbar gasar tamaula ta Sifaniya da suka kece raini ranar Asabar.
Ɗan wasan tawagar Ingila, mai shekara 20 yana da kwallo 10 a raga da ya ciwa Real Madrrid a dukkan fafatawa da ya yi mata a kakar nan.
Bellingham ya fara cin kwallo a minti na tara da fara wasa, sannan ya kara na biyu a zagaye na biyu a karawar.
Vinicius Junior da kuma Joselu suka ci kwallo biyun da Real Madrid ta caskara Osasuna a karawar ta La Liga.
Bellingham wanda ya fara wasa da kafar dama a Sifaniya da fara kakar nan ya ci kwallo a dukkan fafatawa 12, in ban da karo uku da bai yi hakan ba a ƙungiyar da kuma Ingila.
Da za a cire kwallon da Bellingham ya ciwa Real Madrid a kakar nan kawo yanzu to da maki 10 kacal take da shi, bayan wasa tara a La Liga.
Kawo yanzu Real Madrid tana matakin farko a kan teburi mai maki 24, yayin da Barcelona mai maki 20 za ta je gidan Granada a karashen wasannin mako na tara.
Wasannin da za a buga ranar Lahadi:
- Villarreal da Las Palmas
- Atletico Madrid da Real Sociedad
- Deportivo Alaves da Real Betis
- Celta de Vigo da Getafe CF
- Granada da FC Barcelona