Labarai

Balarabe Abbas Lawal – Gajiya ce ta sanya ni faɗuwa a majalisa

Ministan shugaban Najeriya Bola Tinubu, Balarabe Abbas Lawal wanda ya yanke jiki ya faɗi lokacin da ake tantance shi ranar Laraba a zauren majalisar dattijai ya ce gajiya ce ta sanya shi faduwa.

Ministan wanda ya fito daga jihar Kaduna ya faɗi ne bayan ya kammala jawabi game da tarihin rayuwa da karatunsa.

“Yanzu lafiya lau nake ji, an duba ni a asibiti kuma an ba ni magani, gajiya ce kawai, ba wani abu ba ne,” ministan ya shaida wa manema labarai.

Gajiya ce ta sanya ni faɗuwa a majalisa - Balarabe Abbas Lawal

Ministan wanda majalisa ta tabbatar da shi ya fito ne cikin murmushi amma a fuska ana iya gane yana cikin gajiya.

Majalisar dattijai dai ta katse zaman tantancewar da take yi bayan faduwar Balarabe Lawal inda ta koma zaman sirri kafin ta tabbatar da shi tare da sauran wadanda Shugaba Tinubu ya aika sunayensu ga majalisar.