Labarai

BABBAN TASHIN HANKALI: An Tsinci Jariri Sabon Haihuwa A Kano.

INNA LILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN

 

An Tsinci Jariri Sabon Haihuwa A Kano

 

Yanzu aka tsinci wani jariri sabon haihuwa da aka jefar da shi a soron gidan wani mai suna Ibrahim Usama dake Unguwar Goron Dutse bayan gidan Nababa Badamasi dake birnin Kano.

 

Saidai cikin ikon Allah Rariya ta gano yaron yana cikin koshin lafiya, inda aka yi masa wanka tare da suturta shi da kuma yi masa huduba an sa masa suna Muhammad.

 

Yanzu haka an damka Muhammad a hannun Mai Ynguwar Kai Gama.

 

Allah ya raya shi bisa tafarkin Addinin muslunci, Allah ya shiryi wadanda suka aikata wannan rashin imanin.

 

Daga Al’Amin B Kawu (Abu Al’Amin)