Labarai

Ba za mu gudanar da zaɓe ba har sai yanayin tsaro ya inganta – Burkina Faso

Shugaban gwamnatin sojin Burkina Faso ya ce yin zaɓe ba shi ba ne fifikonsu ba a yanzu, kuma ba za a gudanar ba har sai yanayin tsaro ya ingnata.

Kyaftin Ibrahim Traore na waɗannan kalamai ne a jajibirin cika shekara guda da jagorantar kifar da gwamnatin farar-hula.

A baya ya alkawarta gudanar da zaɓen a watan Yulin badi.

A jiya Juma’a, ɗaruruwan mutane suka fito suna gangamin nuna goyon baya ga sojojin da a birnin Ouagadougou.

Wasunsu kuma na riƙe da tutocin ƙasashen da sojoji suka yi wa juyin-mulki na Mali da Nijar.

Yadda yaro ɗan makaranta mai kunya ya zama shugaban ƙasa

Sojoji sun mutu a wani kwanton bauna a Burkina Faso