Labarai

Atiku na son kotun ƙoli ta ba shi damar shigar da sabuwar shaida kan Tinubu

Atiku na son kotun ƙoli ta ba shi damar shigar da sabuwar shaida kan Tinubu

Atiku na son kotun ƙoli ta ba shi damar shigar da sabuwar shaida kan Tinubu

Daga Ahmad Tijjani Bawage

ATIKU ABUBAKAR

Ɗan takarar jam’iyyar PDP a zaɓen shugaban ƙasar Najeriya na 2023, Atiku Abubakar ya buƙaci kotun ƙolin ƙasar ta ba shi damar sabbin hujjoji a ci gaba da matakinsa na ƙalubalantar nasarar shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu.

Wata buƙata da lauyoyinsa suka shigar, ta ce sabuwar shaidar da Atiku ke son gabatar wa kotun za ta tabbatar da zargin da yake yi kan cewa shugaba Tinubu ya yi amfani da takardun bogi a lokacin da yake ƙoƙarin ganin ya fafata a zaɓen shugaban ƙasa.

Atiku Abubakar ya ce wannan abu da Tinubu ya yi na nuna cewa ya aikata laifuka biyu, wato ƙirƙirar takardar kammala karatu ta bogi da kuma zabga ƙarya.

A cewar Atiku waɗannan hujjoji sun ishi kotun ƙoli ta dogara da su wajen cire shugaban ƙasar daga muƙaminsa.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar na so ne kotu ta ba shi wannan dama domin ya miƙa mata takardun shaidar kammala karatu na Bola Tinubu, waɗanda jami’ar jihar Chicago da ke Amurka ta miƙa masa a ranar biyu ga watan Oktoba.