Ana sanar da hukuncin zaɓen gwamnan Kaduna ta manhajar Zoom
Kotu za ta raba gardama kan kujerar gwamnan Kaduna
An fara yanke hukunci
Kotun sauraron kararrakin zaɓen gwamnan jihar Kaduna ta fara sanar da hukunci ta manhajar Zoom.
Tun farko an kafa majigi da kyamarori a kotun, inda daga bisani alƙalai suka bayyana ta manhajar Zoom, suka fara sanar da matsayar kotu.
Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, Isa Ashiru Kudan ne ya shigar da ƙara inda yake kalubalantar zaɓen da aka yi wa Sanata Uba Sani na jam’iyyar APC.
Yayin da ko wane ɓangare ke nuna kwarin-gwiwa na samun nasara a hukuncin da kotun za ta sanar ranar a Alhamis din nan 28 ga watan Satumba 2023, bisa ga dukkan alamu ana zaman kila-wa-kala ne na walau hukuncin ya tabbatar da nasarar ta APC ko kuma akasin hakan.
Tuni aka tsaurara matakan tsaro a sassa daban-daban na jihar don kauce wa afkuwar tashin hankali bayan sanar da hukuncin kotun.
Tun da aka fara sauraron karar a farkon watan Yuni na wannan shekara ta 2023 kan zaɓen da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris 2023, dimbin magoya-baya sukan yi dafifi zuwa kotun domin gani da sauraron yadda karar ke gudana.
A lokacin zaman kotun an rika tayar da jijiyar wuya tsakanin lauyoyin ɓangarorin biyu inda kowa ke kokarin tabbatar da hujjojinsa.
Kowa ne ɓangare na nuna ƙwarin gwiwar nasara a shari’ar
Wasu magoya bayan ɗan takarar na jam’iyyar PDP sun shaida wa BBC cewa hujjojin da lauyoyinsu suka bayar ne ke ba su kwarin gwiwar cewa su za su yi nasara a shari’ar.
Honorabul Bashir Ibrahim Saka-dadi wanda shi ne jagoran yakin neman zaɓen ɗan takarar gwamnan na PDP, ya ce bisa dalilan da suka sa suka je kotu su ne hujjojin da ke hannunsu.
“Kuma mun samu shaidu daga hukumar zaɓe da kayan zaɓe din ya tabbatar da mu a zahirin gaskiya abin da muke kuka gaskiya ne sakamakon zaɓe ya nuna mu muka ci zaɓe,” in ji shi.
Ya ce fatansu shi ne alkalan da suka zauna shari’ar su tabbatar musu da cewa ɗan takarar tasu, Isa Ashiru Kudan shi ne zababben gwamnan jihar Kaduna.
To sai dai shi ma a nashi ɓangaren wanda ake karar, gwamnan jihar ta Kaduna Sanata Uba Sani ya ce yana da kwarin gwiwar shi zai yi nasara kamar yadda sakataren yaɗa labarai na jam’iyyarsu ta APC, Salisu Tanko Wusono ya sheda wa BBC.
“Mu abin da muka kalla da kuma fatanmu shi ne kotu za ta yanke hukunci shari’ar nan ta ba jam’iyyar APC tare da al’ummar jihar Kaduna da suka taru suka zaɓi jam’iyyar da Mallam Uba Sani bisa dalili guda daya” in ji shi.
“PDP duk zaman da aka yi a kotun nan sun kasa bayar da gamsassun hujjoji cewa an yi musu maguɗi a inda suke cewa an yi musu maguɗin,” a cewarsa.
A bisa wannan dalilin ne ya ce suke da imanin kan yadda suka bibiyi shari’ar cewa kotun ba za ta yi wani abu da ya saba wanda suke tsammani na tabbatar musu da nasara ba.