
Shugabar Karamar Hukuma A Jihar Yobe Ta Jagoranci Rusa Gidaje 39 Na Karuwai, Giya Da Ƴan Gala
…ta rushe adadin ɗakuna 140 a gidaje 39
Shugabar karamar hukumar Fika a jihar Yobe Hajiya Halima Kyari Joda ta jagoranci rushe gidajen karuwai, gidajen giya da gidajen ƴan gala har 39 a garin Ngalda dake karamar hukumar Fika.
Kwanakin baya, Hajiya Joda tare da hadin-guiwar sarakunan gargajiya ta jagoranci jami’an tsaro da hukumar Hisba wajen kama masu sana’ar giya, masu gidajen Gala da Gidajen karuwai a garin Ngalda.
Bayan an gurfanar dasu a gaban hukuma, Yau Kuma cikin Ikon Allah ta jagoranci rushe musu gidaje 39 masu dauke da adadin ɗakuna 140.
Hakan ta biyo bayan illar da Gidajen suke yiwa Al’uma musamman wajen lalata tarbiya, safarar miyagun kwayoyi da sauran munanan ɗabi’u da suke haddasawa a cikin al’umma baki daya.