Kasar Iraqi ta rataye wasu mutum uku da aka samu da hannu a harin bam da aka kai a birnin Bagadaza.
Kasar Iraƙi ta rataye wasu mutum uku da aka samu da hannu a harin bam da aka kai a birnin Bagadaza.
Wannan harin bam ya faru ne a cikin shakarar 2016 a cikin watan azumi kuma ya kashe mutane sama da 300 tare da jikkata wasu da dama.
Wannan dai shi ne harin bam mafi muni da aka kai a Iraki tun bayan mamayar da Amurka ta yi a shekara ta 2003.
An aiwatar da hukuncin kisan ne a ranar Lahadi ko Litinin, in ji ofishin Firayim Minista Mohammed Shia al-Sudani.
Amma dai ba a bayyana sunayen wadanda aka kashe ba.
Firaministan ƙasar ya shaida wa iyalan wadanda abin ya shafa cewa an zartar da hukuncin kisa kan mutanen da ke da hannu a tashin bam din.