Labarai

An manta abin tiyata da ya kai girman faranti a cikin wata mata

An manta abin tiyata da ya kai girman faranti a cikin wata mata

An bar wa wata mata wani abin tiyata “da ya kai girman farantin cin abinci” a cikinta a wani asibiti da ke birnin Auckland a New Zealand.

An cire abin tiyatar ne daga cikinta wata 18 bayan ta haihu.

Tun lokacin da aka yi mata tiyatar take fama da raɗaɗi, kuma ta yi ta zuwa wajen likitoci daban-daban domin gano mai yake damunta.

Masu rajin kare haƙƙin ɗan adam sun ce asibitotcin gwamnati ba sa lura da marasa lafiya kamar yadda ya kamata.

Sai dai ma’aikatar lafiya da lura da masu buƙata ta musamman ta yi watsi da wannan lamari, kamar yadda ta bayyana cikin wata sanarwa a ranar Litinin.

“Mutanen da suka yi wannan tiyatar ba za su iya faɗin yadda suka manta da wannan abu a cikinta ba, kuma ba su iya kai wa ga ganin abin ba lokacin da suka kammala tiyatar,” in ji nasarwar.