Labarai

An kama Babban mawaƙi Naira Maley

An kama Babban mawaƙi Naira Maley

‘Yan sandan Sun tsare Azeez Fashola ne wanda aka fi sani da Naira Marley bisa tuhumar da ake masa da hannu a mutuwar Mohbad wani mawaki da yake karkashin wanda ake zargin kafin mutuwarshi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas Benjamin Hundeyin, ya bada sanarwar tsare fitaccen mawakin Najeriya din nan Azeez Fashola wanda aka fi sani da Naira marley.

Naira Marley ya shiga komar ‘yan sandan a jiya Talata ne inda ake sa ran za su masa tambayoyi masu alaka da mutuwar Mohbad wani mawaki mai tashe wanda kafin mutuwar shi ya ke karkashin kamfaninsa kana ake zargin shi da masaniya kan mutuwar mawakin bayan bayyanar wasu faya fayen bidiyon da Mohbad yayi cikin firgici. Duk da cewa ba a alakanta mutuwar Mohbad karara da Naira Marley ba.

Tuni gidakjen radiyo a kudancin Najeriya suka haramta sanya wakokin Naira Marley da mutane ke ganin ya san abin da ya faru da mawakin wanda aka binne shi kashe garin ranar da ya mutu, ba tare da yunkurin gudanar da wani bincike don gano musababin mutuwar shi ba, wani dalili da mutane suke zargin Naira Marley da masaniya game da mutuwar.

Alamu dai sun nuna cewa dangantaka ta yi tsami tsakanin mawakan. An yi mamakin ganin shugaban ‘yan sandan Najeriya IGP Kayode Egbetokun ya bai wa kwamishanan hukumar na Legas umarnin a tono gawarshi domin tabbatar da abin da yayi sanadin mutuwar mawaki.

Ba tare da bata lokaci ba suka aiwatar da umarnin nasa kana aka gudanar da bincike. Tuni dai Naira Marley ya musa zargin da ake masa. Yanzu da ya shiga hannun ‘yan sanda, Naira Marley zai taimamka wa ‘yan sanda da bincikensu. Hundeyin ya bada sanarwar ne ta kafar X wanda a baya aka santa da twitter.