Labarai

An kai wa sojoji hari bayan kashe mutum 60

An kai wa sojoji hari bayan kashe mutum 60

Rundunar sojan Mali ta sake fuskantar hare-hare a sansanoninta kwana ɗaya bayan masu iƙirarin jihadi sun kashe fiye da mutum 60.

 

Rundunar ta ce an kai wa wani ɓangare na filin jirgin saman soja hari, amma ba ta bayar da ƙarin bayani ba.

 

Hukumomi sun ɗora wa ƙungiyoyi masu alaƙa da al-Qaeda alhakin harin na ranar Alhamis.

 

Mazauna yankin sun faɗa wa BBC cewa kwalekwalen ya bar Gao zuwa Mofti a tsakiyar Mali lokacin da aka kai masa harin a Bamba.

 

Wasu daga cikin fasinjoji sun afka ruwa don tsira da rayuwarsu amma kuma suka nitse.

 

Kazalika, maharan sun shiga wani sansanin soja, inda suka kashe dakaru 15, amma rundunar sojan ta ce ta kashe ‘yan bindigar 50.