Labarai

An Ceto Wasu Daliban Jami’ar Gusau Da Aka Sace A Zamfara

An Ceto Wasu Daliban Jami’ar Gusau Da Aka Sace A Zamfara

An Ceto Wasu Daliban Jami’ar Gusau Da Aka Sace A Zamfara

Kawo yanzu dai an ceto dalibai 13 yayin da sauran ke tsare a hannun masu garkuwa.

Jami'ar Tarayya ta Gusau

    • Daga Ishaq Isma’il Musa

Rundunar Sojin Kasa mai yaƙi da ’yan fashin daji a Arewacin Najeriya, ta ce ta samu nasarar kuɓutar da wasu ɗaliban Jami’ar Tarayya da ke Gusau a Jihar Zamfara wadanda ’yan bindiga suka sace da da tsakar daren ranar Asabar 14 ga watan Oktoba.

’Yan bindigar sun far wa ɗakunan kwanan ɗaliban da ke unguwar Sabon Gida, da ke yankin Damba a Karamar Hukumar Gusau, cikin dare a lokacin da daliban suka fara bacci.

Aminiya ta ruwaito cewa ’yan bindigar sun rika harbe-harbe kan mai tsautsayi, lamarin da ya sa suka yi garkuwa da ɗaliban.

Sai dai ckin wata sanarwar da Rundunar Hadarin Daji ta fitar, ta ce rundunar ta samu nasarar kuɓutar da ɗaliban ne bayan da suka mayar da martani a kan lokaci yayin da aka sanar da su halin da ake ciki game da satar ɗaliban.

Sanarwar mai ɗauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar, Kaftin Ibrahim Yahaya, ta ce dakarun sun datse hanyar da suke tunanin ’yan bindigar za su ɓullo, inda suka yi musayar wuta da ’yan bindigar.

“Matsin da ‘yan bindigar suka sha ya tilasta musu tserewa tare da barin ɗaliban,” in ji sanarwar.

A lokacin musayar wutar- wadda aka yi da misalin ƙarfe 12 na dare, dalibai biyu sun samu guduwa da kansu, yayin da jami’an tsaro suka ceto biyu.

A baya- bayan nan ’yan bindiga sun ɓullo da salon kai wa ɗaliban jami’o’i hari tare da sace su a ɗakunan kwanansu.

Ko a watan Satumba ma sai da ’yan bindigar suka kai wa ɗaliban na FUGUS hari a ɗakunan kwanansu inda suka sace ɗalibai masu yawa, wani lamari da ya tayar da ƙura a ƙasar.

Kamfanin Dillancin Labaran na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa a bayan nan an sace dalibai 25 na jami’ar ta FUGUS da kuma wasu ma’aikatan gine-gine 9 a yankin.

Kawo yanzu dai an ceto dalibai 13 da kuma ma’aikatan ginin 3 yayin da sauran ke ci gaba da zaman dan marina a hannun masu garkuwa.