Labarai

An Baiwa Gwamnati Awanni 48 Da Ta Gaggauta Ceto Daliban Jami’ar Gusau.

DA ƊUMI-ƊUMINSA: Wasu Matasa A Jihar Kaduna Sun Baiwa Gwamnati Awanni 48 Da Ta Gaggauta Ceto Daliban Jami’ar Gusau Da ‘Yan Ta@’adda Suka Sa@ce A Jihar Zamfara

 

Daga Comr Nura Siniya

 

Gamayyar ƙungiyoyin matasa a jihar Kaduna ƙarƙashin jagorancin Nazifi Abbas Mai Daraja, sun gudanar da zanga-zanga akan rashin tsa@ron da ya addabi yankin Arewa inda suka yi Allah wadai akan kisan da ƴan bin@diga ke ci gaba da yi ma al’ummar yankin Arewacin Najeriya

 

Mafi akasarin matasan sun yi kira ne ga gwamnatin tarayya da jami’an tsaro da su gaggauta kawo ƙarshen matsalar rashin tsaron da ya addabi yankin Arewa.

 

A cewar matasan ya kamata gwamnatin tarayya ta tashi tsaye wajen kare rayuka da dukiyoyin ƴan Arewa inda suka baiwa gwamnatin Najeriya awa 48 da ta gaggauta ceto ɗaliban jami’ar Gusau da ƴan ta’adda suka sace a ƙwanakin baya.