Labarai

Amurka ta bai wa Ukraine harsashi miliyan daya da ta kwace daga Iran

Amurka ta bai wa Ukraine harsashi miliyan daya da ta kwace daga Iran

Rundunar sojojin Amurka ta ce ta aika da harsashi kimanin miliyan da dubu dari daya zuwa Ukraine, waɗanda ta kwace daga Iran a bara.

 

Bataliyar Amurka da ke sanya idanu kan ayyukan Gabas ta Tsakiya ce ta bayyana hakan, an kwace hasashen ne daga wani jirgin ruwa da aka kama yana nufar Yemen a wata Disamba.

 

Ukraine wadda ke kawance da ƙasashen yamma, ta yi kukan cewa a ‘yan kwanakin nan tana fama a yaƙin da take yin da rashin harsashi.

 

A ranar Litinin ne Centcom ta ce ta aika hasashen da ta kwace daga Iran zuwa Ukraine.

 

Dakarun rundunar sojin ruwan Amurka ne suka kwace harsashan daga wani jirgi da ba a gano na wacce ƙasa ba ne mai suna MARWAN 1 a ranar 9 ga watan Disamba, in ji ta.

 

A watan Yuli Amurka ta ayyana mallakar harsashen ƙarƙashin dokar ‘yan sanda ta kwace abubuwan da ba su dace ba, wacce ke kwace kayayyakin mutanen da aka samu da aikata manyan laifuka.

 

A wannan lamari, an yi iƙirarin cewa kayan mallakin rundunar juyin juya hali ne ta Iran, ƙarƙashin wata tawaga da aka dorawa aikin lura da killace kayyakin gwamnatin ƙasar.

 

Wata sanarwa da rundunar sojin Amurka ta fitar ta ce Amurka “na aiki tuƙuru tare da abokanta da ƙawayenta domin daƙile duk wani taimakon da Iran ke aikewa a yankin ta hanyar da ta dace”.

 

Iran na goyon bayan ‘yan tawayen Houthi a yaƙin da ake yi a Yemen, sai dai kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya haramta aikewa da ƙungiyar makamai ƙarƙashin wata doka ta 2015.

 

An fara yaƙin basasa a Yemen a 2014, lokacin da Houthi ta karɓe iko da Sanaa babban ƙasar ta kuma tuɓe gwamnatin ƙasar.

 

Hamɓararriyar gwamnatin dai ita ce ƙasashen duniya suka sani a Yemen, kuma tana samun goyon bayan tawagar ƙawancen sojin kasashe da Saudiyya ke jagoranta a yankin kazalika da goyon bayan Amurka da na Burtaniya.

 

Tun a tsakiyar bara, ake ta zargin Iran da kai wa Rasha makamai, musamman jirage maras matuƙa, domin amfani da su a yaƙin da take da Ukraine.

 

A ranar Litinin, a wani mataki kan yadda ƙasashen Yamma za su ci gaba da bai wa Ukraine hasashi da ya gudana a Warsaw, Adm Rob Bauer, shugaban kwamitin sojojin ƙungiyar tsaro ta Nato ya ce “duk abin da ake akan idonsu ake yi”.

 

Yace rashin zuba jari na gwamman shekaru na nufin, ko a farkon yakin, rumbur ajiyar hasasai na ƙasashen ƙungiyar tsaro ta Neto ya haura rabi ko ma ya ƙare.

 

Ya ƙara da cewa “akwai buƙatar masana’antu da gwamnatoci su ƙara yawan hasasan da suke samarwa cikin sauri”.