Labarai

Al’ummar Musulmi Suka Gudanar Da Zagayen Mauludin Manzon Allah SAW Zuru Jihar Kebbi.

Yadda Dandazon Al’ummar Musulmi Suka Gudanar Da Zagayen Mauludin Manzon Allah ﷺ A Karamar Hukumar Zuru.

 

Duban-dubatar al’ummar musulmi ne suka gudanar da zagayen Mauludin Manzon Allah ﷺ a karamar hukumar Zuru da ke jihar kebbi.

 

Bikin Mauludin Manzon Allah SAW shine mafi girma acikin dukkan bukukuwa da suke dauke da kamala ta dan Adam bikin na tunawa ne da ranar zagayowar lokacin haihuwar cikamakin Annabawa ne kuma babu kamarsa acikin dukkan bukukuwa na murna ga musulmi.

 

Ranar zuwan Manzon Allah ﷺ duniya itace babbar ranar zuwan mafificin halitta mafi soyuwa a wajen Allah.

 

Muna rokon Allah ya kara muna soyayyar Annabi ﷺ ya karbi rayuwarmu acikin imani alfarmar Manzon Allah (S A W).

 

Daga; Tijjaniyya New Media