Labarai

Abubuwan da ke rage wa ma’aurata sha’awa

Abubuwan da ke rage wa ma'aurata sha'awa

Raguwar sha’awa tsakanin ma’aurata wata matsala ce da ke neman zama ruwan dare game duniya kamar yadda hukumar kula da harkokin lafiyar Ingila (NHS) ta bayyana.

 

NHS ta ce matsalar kan shafi namiji ɗaya cikin biyar, yayin da alƙaluman suka zarta haka tsakanin mata a wasu lokuta.

 

Abubuwa da dama ne suka ke haifar da wannan matsala, kamar yawan aiki ko damuwa da wasu yanayi na rayuwa kamar juna-biyu ko yanayin haihuwa da na shayarwa

 

To sai dai a duk lokacin da matsalar ta auku, likitoci na bayar da shawarar gudanar da bincike domin gano musabbin matsalar a wannan lokaci domin bambancce shi da na sauran mutane, kamar yadda Catarina de Moraes wata ƙwararriyar likitar ƙwaƙwalwa ta bayyana.

 

“A wasu lokuta matsalar rashin shawa’a na da rikitarwa da wahalar sha’ani, domin kuwa matsalar miƙewar azzakari da rashin gamsar da juna yayin jima’i duk alamomi ne na matsalar rashin jin sha’awar saduwa”.

 

Sai dai ba koyaushe ne rashin jin sha’awa ke zama matsala ba.

 

Diego Fonseca, wani ƙwararren likitan kula da irin waɗanna matsaloli ne , ya kuma ce sai alamomin cutar sun kai aƙalla wata shida a jikin mutum sannan za a iya ɗaukarsa a matsayin matsala.

 

“Sai dai ba wani dogon bincike aka yi game da matsalar ba, haka kuma yana da matuƙar muhimmanci a riƙa bincike ga kowanne marar lafiya domin gano abin da ya haddasa masa matsalar,” kamar yadda Catarina de Moraes ta bayyana .

 

Ta hanyar taimakon masana lafiya mun bayyana wasu dalilan da ke haifar da matsalar rashin sha’awa tsakanin ma’aurata.

 

Sauye-sauyen lokutan aiki da yanayin rayuwa

Raguwar sha’awa kan faru ne sakamakon wasu dalilai da mutane kan fuskanta a wasu lokuta kamar damuwa da gajiya da sauye-sauye a wasu muhimman al’amuransu da za su iya shafar lokutan saduwarsu.

 

Alal misali kula da jariri ”Wannan ba lallai ya kasance matsala ba, domin kuwa abu ne da ya zama jiki ga mijin da ke da mace guda.

 

Akan samu raguwar sha’awa a irin wannan yanayi ko da kuwa an kusanci juna.

 

Matuƙar ana samun gamsuwar saduwa, to wannan matsala ba lallai ta kasance ta damuwa ba, kamar yadda Catarina de Moraes ta bayyana.

 

Matsalar ƙwaƙwalwa
Matsalar ƙwaƙwalwa kamar su matsananciyar damuwa da rashin kwanciyar hankali ka iya shafar sha’awa tsakanin ma’aurata.

“Marasa lafiyar da ke da matsalar matsananciyar damuwa ka iya fuskantar raguwar sha’awa sakamakon rashin kwanciyar hankalin ƙwaƙwalwa, lamarin da ka iya haifar da wasu sauye-sauye a ƙwaƙwalwar”, kamar yadda likitar ƙwakwalwar ta bayyana.

A wani bangare kuma wasu magungunan da ake amfani da su domin magance cutar matsanciyar damuwa na haifar da matsalar raguwar sha’awa.

Haka kuma akwai wasu hanyoyin magance irin waɗannna cutuka domin rage illolin da magungunan ke da shi da lafiyar al’umma, kamar sauya magungunan ko rage yawan magungunan da ake sha.

Masana sun yi gargaɗi marasa lafiya da kada su ƙi magance cutar matsalar cutar damuwa matsawar suka gano alamomin cutar a tare da su, domin kuwa rashin magance cutar ka iya shafar ƙarfin jima’insu.

Sun kuma shawarci masu ɗauke da cutar damuwa da su kauce wa amfani da magungunan da ke da hatsari ga lafiyarsu.

“Yana kuma da matuƙar muhimmanci ga marasa lafiya da su riƙa kai rahoton duk wata matsalar da ta shafi jima’i da suke da ita, ga likitocinsu”.

Sauyi a sinadaran halitta
Idan marasa lafiyar ba su da matsalar ƙwaƙwalwa sannan kuma ba su da matsalar sauye-sauyen lokutan aiki da za su iya haifar musu da matasalar rashin sha’awa, abu na gaba da da za a iya dubawa shi ne matsalar sauye-sauyen sidanaran halitta.

Sinadaran Estrogen ga mata da kuma testosterone ga maza, su ne manyan sinadaran da ke kula da karfin sha’awa da jima’i, kamar yadda Caroline Castro wata ƙwararriyar likitan kula da sinadaran halitta a asibitin São Camilo ta bayyana.

Estrogen na ƙunshe da sinadaran da ke ƙara lafiyar al’aurar mata, da ruwan sha’awa da ke fita daga al’aurar mata, da kuma haifar da sha’awa ga mata.

Shi kuwa Testosterone na da alaka da samar da maniyyi ga maza, da kula da lafiyar al’aurarsu da kuma ƙara ƙarfin sha’awa. Sinadarin kan taimaka wajen sanya maza jin sha’awar jima’i.

Magance irin waɗannan matsaloli na da matuƙar wahala, in ji Diego Fonseca.

“Ga maza alal misalai ba iya sinadarin testosterone muke dubawa ba, mukan duba bayanan lafiyarsa ko yana da wata cutar da ka iya haifar masa da wannan matsala”, in ji shi.

Likitoci sun kuma bayyana wani yanayi da ka iya haifar da sauyi a sinadarin halitta kamar juna-biyu ko yanayin haihuwa ko shayarwa kiɓa.

“Ga waɗannan marasa lafiya, akan iya basu magunguna ko shawarwari domin magance matsalolinsu”.

 

Taron-dangin cutuka

Abu na gaba da ke haifar da matsalar kamar yadda likitoci suke yawan yin bayani shi ne haɗuwar cutuka fiye da ɗaya, wanda shi ma ke taimakawa wajen haifar da matsalar rashin sha’awa.

 

Cutukan ƙwaƙwalwa fiye da ɗaya kan shafi ƙarfin sha’awa, lamarin da ka iya haifar da rashin miƙewar azzakari ga maza.

 

Haka ma cutar ciwon suga, ta hanyar haifar da sauyi a sinadaran halitta kan haifar da rashin ƙarfin sha’awa.

 

Sannan kuma mutanen da ke da matsalar cutar zuciya, ka iya fuskantar matsananciyar kasala sakamakon raguwar famfa jini yadda ya kamata daga zuciya.

 

Wannan kasalar kan haifar da raguwar ƙarfin sha’awa.

 

Daɗin daɗawa, wasu magunguna da ake amfani da su wajen magance cutukan zukata ka iya haifar da matsalar rashin shawa’a.

 

Hanyar kauce wa matsalar

Likitocin da aka tuntuɓa game da matsalar sun bayyana cewa babu wata takamammiyar hanya ta magance matsalar.

 

Saboda a cewarsu kowane marar lafiya da maganin da ake ba shi ya dogara ne kan abin da ya haddasa masa cutar.

 

Wata shawara da likitoci ke bayarwa game da cutar, ita ce ya kamata ma’auratan su riƙa tuntuɓar junansu da zarar sun fara jin matsalar a jikinsu.

 

“Yana da matuƙar muhimmanci a samu fahimtar juna kan matsalar, koda kuwa hakan zai haifar da saɓani tsakanin ma’auratan.

 

Yin magana game da raguwar sha’awa kan taimaka wajen magance matsalar rajin jituwa tsakanin ma’aurata tare da bayar da dama ga ma’aurata su fahimci yanayin da ɗayansu ke ciki domin daukar matakin magancewa tare,”in ji Diego Fonseca.