Labarai

Abubuwan da aka cimma a tattaunawar ‘yan kwadago da gwamnatin Najeriya

Abubuwan da aka cimma a tattaunawar ‘yan kwadago da gwamnatin Najeriya

A ranar Lahadin da ta gabata ne gwamnatin Najeriya ta yi wani zama na musamman da shugabannin kungiyar kwadago na kasar NLC da TUC, kan matakan da za a dauka na magance takaddamar da ta biyo bayan cire tallafin man fetur da ake ta takaddama a kai.

 

Su dai ‘yan kwadagon sun shirya tafiya yajin aikin sai baba ta gani a wannan makon yayin da ake tsaka da bikin cikar kasar shekara 63 da samun ‘yancin kai.

 

Sai dai yayin wani zama da shugaban ma’aikatan fadar shugaban Najeriya Femi Gbajabiamila ya jagoranta tare da shugabannin kwadagon, an tattauna muhimman batutuwa don lalubo mafita.

 

Batutuwan da aka tattauna sun hadar da amincewa da karin albashin wucin gadi na Naira 25,000 ga ma’aikata, da kuma gaggauta samar da motoci masu amfani da gas don saukaka matsalolin sufuri, da cire tallafin man ya haifar.

 

Wani alkawari kuma da gwamnatin ta yi shi ne na samar da kudade ga kananan masana’antu, da kuma cire harajin VAT daga iskar gas tsawon watanni shidda, da rabawa gidaje miliyan 15 tallafin Naira dubu saba’in da biyar a wata uku, ma’ana Naira dubu ashirin da biyar a kowanne wata.

Matsayar da aka cimma

Yayin taron na shugabannin kwadagon da kuma bangaren gwamnati dai an amince a kan cewa ba za a iya aiwatar da dukkan wadannan manufofi ba, a yayin da ‘yan kwadago ke yajin aiki, don haka har sai sun janye yajin aikin da suke so su tafi.

 

Kazalika shugabannin kwadagon sun bukaci a sake duba karin da aka yin a naira dubu ashirin da biyar, don haka wakilan gwamnati a zaman sun ce za su sake mika wa shugaba Tinubu bukatar don ya yi nazari a kanta.

 

Gwamnatin Tarayya za ta fara biyan N75,000 ga gidaje miliyan 15 akan naira 25,000 duk wata, na tsawon watanni uku daga Oktoba zuwa Disamba 2023.

 

An cimma matsaya a kan cewa za a kafa wani karamin kwamiti da zai tabbatar da aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma, kana kungiyoyin na NLC da TUC za su yi nazari a kan tayin da Gwamnatin Tarayyar ta yi, da manufar fasa tafiya yajin aiki.

 

Sauran wadanda suka wakilci gwamnatin Najeriya a zaman sun hadar da Ministan Kudi kuma Ministan Tattalin Arziki, Wale Edun, da Ministan Yada Labarai da Wayar da kan jama’a Mohammed Idris, da Ministan Kwadago Simon Lalong, da Karamin Ministan Kwadago, Nkeiruka Onyejeocha, da Ministan Kasafin Kudi da Tsare Tattalin Arziki, Abubakar Atiku Bagudu, Ministar Agaji da ta Yaki da fatara Betta Edu, da Ministan ciniki da Masana’antu da Zuba Jari, Doris Uzoka-Anite, da Shugaban Ma’aikata na Tarayya, Dr. Folasade Yemi- Esan da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Mallam Nuhu Ribadu.