Labarai

Abubuwa biyar da Najeriya ta kasa magancewa tun bayan samun ƴancin kai

Abubuwa biyar da Najeriya ta kasa magancewa tun bayan samun ƴancin kai

Najeriya ta cika shekara 63 da samun ƴancin kai a ranar ɗaya ga watan Oktoban 2023, kasancewar ta samu ƴancin ne a ranar ɗaya ga watan Oktoban shekarar 1960.

 

Lamarin na zuwa ne yayin da ƙasar ke da jaririyar gwamnati, wadda aka ƙafa a ƙasa da shekara guda ƙarƙashin shugaban ƙasa na 16, Bola Ahmed Tinubu.

 

Duk da ƙalubalen da ta samu tun bayan samun ƴancin kai, ana ganin cewa ƙasar ta cimma nasarori da dama, kamar ci gaba da kasancewarta ƙasa dunƙulalliya da kuma komawa tafarkin dimokuradiyya.

 

Sai dai akwai wasu ƙalubalai da dama da ake ganin ta gaza cimmawa, kamar gaza kawar da talauci, rashin inganta ɓangaren masana’antu da rashin isasshiyar wutar lantarki.

 

A ɓangare ɗaya kuma masana, kamar Farfesa Tukur Abdulkadir na jami’ar jihar Kaduna, da kuma Dakta Shu’aibu Shehu na gidan adana kayan tarihi na Arewa House da ke Kaduna na ganin cewa akwai wasu manyan matsaloli da ke yi wa ci gaban ƙasar ƙafar ungulu tun bayan samun ƴanci, waɗanda har yanzu ta gaza magancewa:

 

Rashin yarda da juna

Tun gabanin samun ƴancin kan ƙasar alamu sun nuna cewa akwai rarrabuwar kawuna tsakanin manyan ɓangarori uku na ƙasar – Arewaci da Yammaci da kuma Kudu maso gabas.

 

Sai dai lamarin a wancan lokaci bai yi ƙamari ba kasancewar kowane yanki na cin gashin kansa ne.

 

Sai dai bayan samun ƴancin kai lamarin ya fara fitowa fili kuma ya riƙa ƙamari har zuwa lokacin da aka yi juyin mulkin 15 ga watan Janairun 1966.

 

A wannan juyin mulki ne aka kashe firaminista Abubakar Tafawa Balewa, da wasu manyan ƴan siyasa da sojojin ƙasar.

 

An riƙa kallon lamarin a matsayin wani yunƙuri na kawar da al’ummar wani ɓangaren ƙasar daga shugabanci.

 

Wannan da kuma abubuwan da suka biyo baya ne suka ƙara fito da rashin yarda da juna ƙarara tsakanin al’ummar ƙasar.

 

Wani lamari da ya kai ga yaƙin basasar ƙasar wanda aka gwabza daga watan Yulin 1967 zuwa Janairun 1970.

 

Farfesa Tukur Abdulkadir ya ce “da farko bayan yaƙin basasa za a iya cewa an fara amincewa da yarda da juna, babu matsala ta ƙiyayyar ƙabilanci da addini to amma abin takaicin tun ƙarshen ƙarni na 20 wannan al’amari ya fara dawowa, har yau kuma ba a iya magance shi ba.”

 

Ya ce irin waɗannan abubuwa ne suka haddasa rikici na addini da aka samu jihar Kaduna, kamar rikicin Zangon Kataf a shekarar 1992, da kuma rikicin shari’a da aka samu a shekarar 2000.

 

Sai kuma rikice-rikice na ƙabilanci a jihar Filato, waɗanda aka fara samu tun daga shekarar 2001.

 

Farfesa Tukur ya ce har yanzu wannan matsala na nan an kasa magance ta a Najeriya, kuma rarrabuwar kawuna na ƙaruwa a tsakanin al’umma.

 

A yanzu haka dai akwai ƴan awaren IPOB masu rajin kafa ƙasar Biafra, waɗanda ke iƙirarin cewa ana nuna musu wariya.

 

Sannan ko a shekaru biyu da suka gabata an samu ƙarin kiraye-kiraye daga masu iƙirarin kishin ƙasar Yarbawa a kudu maso yammacin ƙasar.

 

Baya ga ƴan ƙungiyar Boko Haram a arewa maso gabas waɗanda gwamnatin da ta gabata ta ce ta ci galabar su.

 

Zaɓe maras inganci

 

Zaɓe maras inganci

Farfesa Tukur Abdulkadir ya ce tun daga jamhuriya ta ɗaya har yanzu ba a iya gudanar da zaɓen da ya zamo karɓaɓɓe ga kowa ba.

 

Ya ce a lokacin jamhuriya ta biyu, Chief Obafemi Awolowo sai da ya shigar da ƙara bayan zaɓen da ya bai wa Alhaji Aliyu Shagari nasara.

 

Haka nan ma a shekarar 1983, an zargi jam’iyyar NPN mai mulki da yin murɗiya a zaɓen da aka gudanar, wani abu da ya haifar da tangal-tangal a ɓangaren siyasa, inda a ƙarshe aka yi wa gwamnati mai ci a lokacin juyin mulki.

 

A jamhuriya ta uku ma ƙasar ta shiga ruɗani, inda hatta zaɓuka na fitar da ƴan takara suka ci tura, sannan kuma daga ƙarshe gwamnatin mulkin soja ta janar Ibrahim Badamasi Babangida ta rushe zaɓen da aka fafata tsakanin marigayi Moshood Abiola da Alhaji Bashir Tofa na ranar 12 ga watan Yuni, 1993, wani abu da ya jefar ƙasar cikin ruɗani.

 

A cewar Farfesa Tukur “haka nan an samu kwamacala a zaɓukan 2003 da 2007 da kuma 2011.” Haka nan ma a 2015 inda sai da aka je kotu tsakanin Atiku Abubakar da Muhammadu Buhari kan sakamakon zaɓen.

 

Sai kuma shekarar 2023, inda yanzu haka jam’iyyun adawa guda uku suka garzaya kotu suna neman a soke nasarar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

 

Rashin kyakkyawan shugabanci

 

Rashin zaɓe mai inganci za a iya cewa shi ne tushe na rashin samun kyakkyawan shugabanci.

 

Kusan a tsawon shekarun da Najeriya ta samu ƴanci a duk lokacin da aka samu sauyin gwamnati akan faɗa ne cikin halin ‘gwara jiya da yau’.

 

Wato ana ganin cewa shugabannin da suka gabata sun fi waɗanda suka zo daga baya kishin ƙasar da ci gabanta.

 

Har ta kai ga cewa Dr Shu’aibu Shehu ya ce “muna da shugabanni ne waɗanda kansu kawai suka sani.”

 

Ya bayyana cewa irin waɗannan shugabanni ba su damu da inganta rayuwar al’umma ba sannan kuma sukan kwashe kuɗi su kai ƙasashen ƙetare.

 

Rashawa da cin hanci

Tun a jamhuriya ta farko, sojojin da suka yi juyin mulki sun yi wa ƴan siyasa zargin rashawa, sai dai a cewar Farfesa Tukur “alƙaluma da suka bayyana kusan za a iya cewa sun nuna babu abin da ya tabbatar da haka, saboda babu wani abu da (shugabannin) suka tara ko suka bari wa iyalai ko makusantansu.”

 

Sai dai abubuwan sun riƙa taɓarɓarewa tun daga wancan lokaci.

 

Farfesa Tukur ya ce lamarin ayyukan rashawa ya ƙara ta’azzara da ƙazancewa a Najeriya musamman daga baya-bayan nan, inda shugabannin ke kallon mulki a matsayin wata dama ta azurta kai.

 

Ko gwamnatin da ta gabata ta Muhammadu Buhari, ɗaya daga cikin manyan alƙauwrran da ta yi a lokacin yaƙin neman zaɓe shi ne batun yaƙi da rashawa.

 

Sai dai har zuwa wannan lokaci ana nan jiya-i-yau, babu wani ci gaba da aka samu wajen yaƙi da matsalar ta cin hanci da rashawa a Najeriyar.

 

Fashi da makami

 

A cewar Farfesa Tukur, fashi da makami wani abu ne da a can baya ake kallon shi a matsayin matsala ta wani ɓangare guda ɗaya.

 

Lamarin ya fi faruwa ne a yankin kudu maso gabas, sai kuma kudu maso yamma daga bisani.

 

Wannan lamari ne ya rikiɗe zuwa batun garkuwa da mutane.

 

A cewar Farfesa Tukur “a baya ana kallon matsalar kamar wasa kuma a matsayin ta yankin kudu kaɗai, to amma yanzu ga shi ta zo ta shafe mu muma. Kuma wannan ne ya haifar da ƙarin matsalolin tsaro na ƙarni na 21.”

 

Ya bayyana cewa rashin ɗaukar matakin kawar da matsalar ta fashi da makami ya sanya yanzu an samu wasu matsalolin kamar na rikicin manoma da mikyaya da kuma garkuwa da mutane a ilahirin faɗin ƙasar.

 

Mece ce mafita?

 

Masanan na ganin cewa duk da tsawon lokacin da aka kwashe ana fama da waɗannan matsaloli akwai hanyoyin da za a iya bi wajen ganin an ci galabar su.

 

Ɗaya daga ciki shi ne a bar dimokuraɗiyya ta ɗore, ta hanyar ƙyale ƴan siyasa su riƙa warware matsalolinsu da kansu, ba tare da katsalandan na sojoji ba.

 

Farfesa Tukur ya ce barin ƴan siyasa su warware matsaloli zai sa a kai wani lokaci da siyasar za ta zamo tana da tsafta.

 

Haka nan kuma ya kamata shugabanni su riƙa kallon muƙaman da suke kai a matsayin wata dama ta hidimta wa al’umma.

 

Malamin jami’ar ya ce “shugabanni a yanzu na kallon shugabanci a matsayin dama ce ta a kece raini, da azurta kai ko ƙabilar da yankin da aka fito ko a kyautata wa surukai ko ƴaƴa ko dangi.”

 

Haka nan Farfesan ya ce ya kamata a riƙa zaɓen shugabanni bisa cancanta.

 

“A baya zaɓen mutane ake yi ba don suna so ba, ana zaɓen su ne saboda cancanta. Ta irin haka ne aka zaɓi mutane irin su Abdulƙadir Balaraben Musa da irin su Abubakar Rimi.” In ji shi.