Labarai

Abin da ya kamata ku sani kan wasan Arsenal da Man City

Abin da ya kamata ku sani kan wasan Arsenal da Man City

Abin da ya kamata ku sani kan wasan Arsenal da Man City

Premier League

ASALIN HOTON,GETTY IMAGES

Kociyan Manchester City, Pep Guardiola ya ce Arsenal za ta dade ana damawa da ita a gurbin masu neman lashe Premier League a kowacce kaka.

Arsenal, wadda ta yi ta biyu a bara biye da Manchester City ta yi wasa bakwai a Firimiya ba tare da an doke ta ba kawo yanzu.

Ita kuwa City ta yi rashin nasara a hannun Wolverhampton a karawar mako na bakwai a babbar gasar tamaula ta Ingila.

”Abokiyar hamayya ce a bara za kuma su dade a wannan gurbin.” in ji Guardiola.

An tambaye shi ko Arsenal za ta iya daukar kofin bana, sai ya kara da cewar: ”Hakika da ita da Liverpool.

Idan za ka tantance wadanda za su iya lashe kofin bana sai bayan kammala wasa 10 da fara kakar nan. Ya kamata mu dan jira, amma manyan kungiyoyi kullum ana sa musu rai.

”Arsenal ta koma kan turba. Lokacin da nake mataki da na fara horar da tamaula a Barcelona na san cewar mun yi tata burza da Sir Alex Ferguson a Manchester United.

”Duk lokacin da ka duba jadawali da cewar za ka je filin Emirates, lallai kasan da akwai aiki a gabanka.

Arsenal ta kasa cin wasa 12 da ta fuskanci City a karawar da suka yi a baya, karon farko da ta kasa cin City tun 2015.

Gunners ta yi nasara a kan Manchester City a Community Shield a bugun fenariti gabanin fara gasar Premier League ta bana – Mikel Arteta na fatan za su kara kwazo a fafatawar da zai yi da City ranar Lahadi.

”Fargabata ita ce kwazon da kungiyar da za mu fuskanta take kai, dole sai mun kasance cikin ganiya 100 cikin 100,” in ji Arteta

”A irin wannan wasan kana bukatar gogaggun ‘yan kwallo masu kwarewa, shi ne za ka samu sakamakon da kake bukata.

Labarin da ya shafi kungiyoyin biyu:

Premier League

ASALIN HOTON,GETTY IMAGES

Ana cewa da kyar idan dan wasan Arsenal, Bukayo Saka zai kara a wasan, wanda ya ji rauni a Champions League da Lens ta yi nasara, amma wasu na cewa ya murmure.

Gabriel Martinelli zai ci gaba da jinya, wasa na shida ke nan da Gunners za ta yi ba tare da shi ba.

Ita kuwa City za ta buga karawar ba tare da Rodri ba, wanda wasa na uku ke nan da zai kammala hukuncin dakatar da shi da aka yi.

Bernardo Silva ya warke, wanda ya buga wa City wasa ranar Laraba, yayin da har yanzu John Stones da Kevin de Bruyne ke jinya.

Karawa tsakanin kungiyoyin:

Arsenal ta yi rashin nasara a wasa 15 daga 16 har da rashin nasara 12 a jere a hannun City a Premier League.

Wasa biyu da Arsenal ta doke City shi ne a FA Cup karawar daf da karshe da cin 2-0 a 2020 da kuma 2-1 a 2017

Arsenal ta yi fafatawa 16 da Manchester City amma kwallo na shiga ragarta.

City ce kadai kungiyar da Mikel Arteta ya kasa yin nasara a matakinsa na koci a Premier League, wanda aka ci dukkan wasa bakwai da ya fuskanci Guardiola.

Arsenal

Bukayo Saka

ASALIN HOTON,GETTY IMAGES

Har yanzu Arsenal ba ta yi rashin nasara ba a Premier League, wadda ta ci wasa biyar da canjaras biyu daga karawa bakwai da ta yi.

To sai dai a karon farko a bana an ci Arsenal, shi ne wanda ta yi rashin nasara 2-1 a hannun kungiyar Faransa a Champions League.

Gunners ta yi nasara 19 daga 26 a Premier League a gida da canjaras biyar da rashin nasara a hannun Manchester City da kuma Brighton.

Arsenal ta barar da maki biyar a wasa takwas a Premier a gida ba tare da Bukayo Saka ba da cin fafatawa uku da canjaras uku aka doke ta a biyu.

Saka yana da hannu a cin kwallo biyar da bayar da biyu aka zura a raga a karawa takwas a Premier League.

Manchester City

Erling Haaland

ASALIN HOTON,GETTY IMAGES

Watakila Manchester City ta yi rrashin nasara biyu a jere a Premier League a karon farko tun Disambar 2018, lokacin da Crystal Palace da Leicester City suka doke ta.

Erling Haaland ya ci Arsenal kwallo a dukkan karawar da suka yi a bara, wanda ya zura kwallayen a raga bayan minti 80.

Haaland ya zura kwallo a raga a wasa hudu baya a Premier League da ya buga a Landan, wanda ya fara daga lokacin da City ta ci Arsenal 3-1 a Fabrairu.

Mai tsaron raga, Ederson zai buga wasa na 300 a City idan an saka shi fafatawar hamayyar ta ranar Lahadi..