Labarai

Wasu Kungiyoyi Sun Kona Jar Hula Tare Da Amincewa Da Korar Kwankwaso A NNPP.

Ƙungiyoyin magoya bayan NNPP a Katsina sun amince da korar Kwankwaso tare da shan alwashin ƙona jar hula

 

Gamayyar ƙungiyoyin magoya bayan jam’iyyar NNPP a jihar Katsina sun amince da korar tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar Najeriya Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso daga jam’iyyar tare da shan alwashin nesanta kansu da hotunansa da kuma ƙone duk wata jar hula dake tare dasu.

 

Wannan na ƙunshe a cikin wata sanarwa da shugaban gamayyar ƙungiyoyin magoya bayan NNPP na jihar Katsina Alhaji Ibrahim Isyaku ya fitar a ranar Litinin 10 ga watan Satumba, 2023.

 

Biyo bayan zargin da suke yi wa Kwankwaso na karkatar da kuɗaɗen da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar NNPP reshen jihar Katsina suka tara, inda ya yi amfanin kansa da kuma ɗaukar ɗawainiyar zaben jihar Kano da kuɗaɗen.

 

Isyaku, ya kuma jaddada goyonsa kan matakin da kwamitin amintattu na NNPP ya ɗauka na ficewa daga yarjejeniyar MOU da ƙungiyoyin Kwankwasiyya da TNM suka rattaba hannu a kai.

See Also  Menene gaskiyar labarin da ake yadawa, na farashin Man Fetur zai koma Naira 250 ko 300 a sati mai zuwa?

 

Haka zalika ya yi fatali da yunƙurin da ake yi na ruguza wanda ya assasa NNPP, Dokta Boniface O Aniebonam.