Labarai

Ƴan sanda sun kama mutum 29 da zargin aikata dabanci a Kano

Ƴan sanda sun kama mutum 29 da zargin aikata dabanci a Kano

Rundunar ƴan sanda a jihar Kano, ta ce ta kama ƴan daba 29 waɗanda ake zargi da tayar da hargitsi a lokacin bikin Takutaha na bana.

 

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ƴan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta ce sun ƙwato wuƙaƙe masu kaifi guda 19, da ƙwayoyi da almakashi 2 da kuma dutsen guga 2.

 

Kiyawa ya kuma ce mutum 222 waɗanda ake zargi da aikata laifuka daban-daban sun tuba tare da miƙa wuya.

 

Ya ce tubabbun ƴan daban na aiki da ƴan sanda domin samar da zaman lafiya a faɗin jihar Kano.

 

Kiyawa ya ƙara da cewa sun kuma samu nasarar kama waɗanda ake zargi da aikata fashi da makami guda 28, waɗanda ake zargi da garkuwa da mutane guda takwas, da motoci 10 da babura takwas da sauransu.