Labarai

Ƴan bindiga sun sace ɗaliban Jami’ar Nasarawa

Ƴan bindiga sun sace ɗaliban Jami’ar Nasarawa

Ƴan bindiga sun yi awon-gaba da ɗalibai huɗu na jami’ar jihar Nasarawa da ke garin Keffi.

 

Bayanai sun nuna cewa an sace ɗaliban ne ranar Talata a lokacin da wasu ƴan bindiga suka kai samame a gidajen kwanansu da ke Anguwar Kare, a karamar hukumar Keffi.

 

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴan sanda a jihar, DSP Ramhan Nansel, ya tabbatar da lamarin a wata tattaunawa ta wayar tarho.

 

Ya ce da sanyin safiyar Talata ne rundunar ƴan sanda a jihar ta samu kiran gaggawa cewa wasu ƴan bindiga sun kai hari a wani gida a Anguwar Kare.

 

“Rundunar tana sane da sace mutanen da aka yi da misalin karfe 12:55 na dare yayin da aka samu rahoton cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka mamaye wani gida da ke Anguwar Kare, Keffi,” inji Nansel.

 

Kokarin da aka yi na bin sawun wadanda suka aikata laifin ya ci tura amma an fara farauta domin kuɓutar da ɗaliban, in ji kakakin ‘yan sandan.