Labarai

Ƙurar da ta taso a Najeriya kan zargin rusa Babban Masallacin Ƙasa

Ƙurar da ta taso a Najeriya kan zargin rusa Babban Masallacin Ƙasa

Wata taƙaddama ta taso cike da zarge-zarge na yunƙurin ƙwace fili, da kuma rushe sashen hamshaƙin Babban Masallacin Ƙasa na Abuja. Lamarin dai ya “janyo tunzuri da ɗar-ɗar a zukatan Musulman Najeriya da ma na ƙetare”.

 

An yi ta tada jijiyoyin wuya da kumfar baki, musamman a shafukan sada zumunta game da wannan batu a kan katafaren ginin tarihin na ibadar Musulmai .

 

Wasu sun riƙa yayata cewa Nyesom Wike, ministan Abuja ne ya ba da umarnin rushe sashen Babban Masallacin, da kuma ƙwace fulotan masallatan Abuja ciki har da na masallacin na ƙasa.

 

Haka kuma akwai masu cewa sabon ministan ya taɓa aikata irin haka, ga wani masallaci a birnin Fatakwal lokacin da yake gwamna a jihar Ribas.

 

Mista Wike dai ya musanta duk zarge-zargen nan. Ya ma yi alƙawarin cewa, “Idan ba mu fi masu mulkin baya taimaka wa (Babban Masallacin) ba, to za mu ci gaba da yin daidai su”.

 

”Don haka, ya kamata mutanenmu su daina cewa ana cungunawa wata ƙungiya ko wani addini ko kuma wata ƙabila.”

 

Shi ma kwamitin gudanarwa na Babban Masallacin, a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, ya ce rahotannin rushe wani ɓangare na masallacin da aka yi ta yayatawa, ba gaskiya ba ne.

 

Sanarwar ta ce babu wani lokaci, yayin ganawar ministan Abuja da shugaban kwamitin gudanarwar masallacin, Mai martaba Etsu na Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar, da aka ambaci batun rushe wani ɓangare na Babban Masallacin na Ƙasa.

 

Daga ina batun rusa masallaci ta ɓullo?

Zargin rusa Babban Masallacin na Abuja, ga alama ya taso ne sanadin batutuwa guda biyu da suka danganci babban wurin ibadar na Musulmai da ke tsakiyar babban birnin tarayyar.

 

A watan Satumba ne kafofin labaran Najeriya suka ambato Nyesom Wike yana bai wa masu fulotai kimanin 200 a tsakiyar Abuja, wa’adin wata uku su fara ginawa, ko kuma su fuskanci yiwuwar soke ikon mallaka da aka ba su.

 

Matakin da mai yiwuwa zai shafi wuraren ibada da dama a birnin, ciki har da babban masallaci na ƙasa.

 

Ana haka ne kuma, sai maganar aikin faɗaɗa wani titi mai maƙwabtaka ya taso, wanda rahotanni suka ce sai an buƙaci wani sashe na Babban Masallacin Abuja, don cimma burin da yin haka.

 

Da yake jawabi, lokacin da kwamitin Babban Masallacin a ƙarƙashin jagorancin Etsu na Nupe, ya kai wa Nyesom Wike ziyara ranar Laraba, ministan Abuja ya ce sun ƙara wa’adi a kan wata uku, ga cibiyoyin addinai, su gina fulotan da suka mallaka a birnin.

 

Kwamitin dai ya ziyarci ministan ne don fayyace bayani a kan matsayin fulotan Babban Masallacin na Ƙasa, da dambarwa ta taso a kansu.

 

Nyesom Wike ya ce umarnin soke ikon mallakar fulotai da gine-ginen da aka yi watsi da gina su nan da wata uku, da ya bayar, ba a yi shi don cusgunawa wasu ɗaiɗaikun mutane ko ƙungiyoyi ba.

 

A cewarsa, manufar an ɓullo da ita ne don a canza tsarin Abuja, kuma a hana ɓata-gari amfani da irin waɗannan wurare a matsayin mafaka.

 

Me Wike da Babban Masallaci na Ƙasa suka cimma?

 

Kwamitin Babban Masallaci na Ƙasa ya bayyana a cikin sanarwar da ya fitar cewa jami’an gudanarwar masallacin ƙarƙashin Mai martaba Etsu na Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar sun cimma yarjejeniya uku tare da ministan Abuja, a ziyarar da suka kai masa ranar Laraba.

 

Yarjejeniyar dai ta shafi fulotan masallacin guda biyu da kuma aikin yi wa wurin ibadar gyaran fuska.

 

Gina fuloti mai lamba 99

Kwamitin dai ya yi wa Minista Nyesom Wike bayani a kan ƙoƙarin mahukuntan masallacin wajen gina fulotin. Etsu na Nupe ya shaida masa cewa tuni Babban Masallacin ya samu amincewar hukumar raya birnin Abuja a kan tsarin ginin da za a yi a wurin.

 

Babban basaraken ya nemi ƙarin lokaci daga ministan don Babban Masallacin ya samu halin gina fulotan da hukumomi suka mallaka wa wurin ibadar.

 

Wike ya ce ”Mun san halin da ƙungiyoyin addinai suke ciki, abin da suke samu taƙaitacce ne, tun da su ba wuraren kasuwanci ba ne.

 

“A irin wannan ɓangare, muna iya cewa bisa masalaha ta addini, maimakon wata uku, muna iya ba da ƙarin lokaci.”

 

Gina fuloti mai lamba 63

Sanarwar Babban Masallacin ta ambato Etsu na Nupe yana faɗa wa Nyesom Wike cewa an sanar da hukumomin Babban Masallacin cewa wani makeken sashe na fulotin masallacin mai lamba 63, zai shiga cikin aikin faɗaɗa titi da gwamnati ta ƙuduri aniyar yi.

 

Rahotanni sun ambato cewa an kusa fara aiki a kan fulotin wanda ke daura da Cibiyar ‘Yar’adua, kafin a bai wa masallacin sanarwar ya ‘dakatar da aiki’.

 

Don haka, shugaban kwamitin gudanarwar ya nemi sanin matsayin fulotin a yanzu, da kuma ragowar da ya rage, wanda za a sake mallakawa masallacin, da madadin da ya dace a bai wa Babban Masallacin na Ƙasa.

 

“Kuma amsar da Mai girma minista ya bayar, tana da daɗi,” in ji sanarwar

 

Yi wa masallacin gyaran fuska

Abu na ƙarshe kuma shi ne masu ziyarar sun kuma nemi tallafi don ci gaba da aikin gyaran fuska ga Masallacin na Ƙasa, wanda hukumar raya birnin tarayya ke gudanarwa tun kafin hawan gwamnatin Tinubu.

 

Shugaban kwamitin ya nunar cewa Shugaba Olusegun Obasanjo ne, wanda ya ɓullo da tsarin kafa gidauniya don yi wa masallacin gyaran fuska, ya amince da ɗaga martaba Babban Masallacin na Ƙasa zuwa matsayin muhimmin ginin tarihi na ƙasa.

 

Haka kuma, rahotanni sun ambato Wike na bai wa hukumar raya birnin Abuja umarnin ta gaggauta sanar da shi game da matsayin Babban Masallacin na Ƙasa da kuma shirin diyya da aka tanadi biya kan fulotan nasa.

 

Batun addini dai yana da matuƙar sammatsi da saurin haifar da tashin-tashina a Najeriya, sau da yawa kuma akan zargi ‘yan siyasa da rura wutar ƙaramar dambarwa a ƙasar da ke da yawan rarrabuwar kai.